Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

17 Faburairu 2024

07:13:23
1438365

Ikrarin Janar Din Yahudawan Kan Kwarewar "Sayyid Hassan Nasrallah" Da Kuma Karfin Hizbullah.

Wani Janar na gwamnatin sahyoniya mai ritaya ya tabbatar da karfin kungiyar Hizbullah da kwarewar " Sayyid Hassan Nasrallah" babban shugaban kungiyar Hizbullah a kasar Labanon.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – ABNA- ya bayar da rahoto cewa: "Gershon Hakohin", birgediya janar na gwamnatin sahyoniya mai ritaya, ya ce Sayyid Hassan Nasrallah, babban shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yana da hikima kuma a lokaci guda cikin kwarewa da kuma hatsari.

Ya kara da cewa: Nasrallah yana da kwarin gwiwa na goyon bayan Hamas da kuma kokarin amfani da yanayin da ake ciki wajen mayar da kungiyar Hizbullah ta zamo mai ikon karfi a yankin gabas ta tsakiya.