Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

17 Faburairu 2024

06:42:45
1438356

Sojojin Yahudawan Sahyoniya Sun Kai Sumamen Kamu A Yammacin Gabar Kogin Jordan

Kafafen yada labarai sun bayar da labarin irin gagarumin farmakin da yahudawan sahyuniya suka kai a sassa daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan da kuma kame 'yan kasar Falasdinu ba tare da wasu dalilai masu ma'ana ba.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) – ABNA- ya bayar da rahoto bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Quds (Qudsana) inda shima ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera cewa, a safiyar yau ne sojojin yahudawan sahyoniya suka kai hari a kauyen Nasariyeh da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

A cikin wannan harin, ‘yan sahayoniyawan sun kai farmaki gidajen wasu ‘yan kasar Falasdinu da ke zaune a yammacin gabar kogin Jordan tare da bincike wadannan gidajen.

Kafafen yada labaran Falasdinu sun kuma bayar da rahoton cewa, sojojin mamaya na yahudawan sahyoniya sun kai hari a yankin Barta da ke kudu maso yammacin Jenin, tare da kame wasu ma'aikata da dama daga zirin Gaza da ke zaune a wannan yanki.

Kauyen Burin Iraki, dake kudancin birnin Nablus, shi ma ya fuskanci wani hari da sanyin safiya da 'yan sahayoniya suka kai daga yankin arewacin wannan kauyen. Sojojin yahudawan sahyoniya tare da kayan aikinsu sun kai hari a sabon yankin Nablus da Hajja da ke gabashin Qalqilya a gabar yammacin kogin Jordan.

Haka nan kuma sojojin mamaya sun kai hari a kauyukan Skaka da Yasuf da ke cikin yankin Salfit da kuma yankin Qiblan a kudancin Nablus.

Hukumomin shari'a na Falasdinu 2 sun sanar a baya a cikin wani rahoto cewa adadin Falasdinawa da ke zaune a yammacin gabar kogin Jordan da sojojin yahudawan sahyuniya suke tsare da su tun ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata da kuma fara farmakin guguwar Al-Aqsa ya karu.

Kwamitin kula da fursunoni da kungiyar fursunoni ta Falasdinu sun bayyana a cikin wannan rahoton cewa adadin Falasdinawa da sojojin yahudawan sahyoniya suka kame a yammacin gabar kogin Jordan tun ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ya kai kimanin mutane 7020.