Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

12 Faburairu 2024

06:24:34
1436975

Hamas Ta Ce Kisan Kiyashin Da Isra'ila Ke Yi Na Nufin Tilastawa Falasdinawa Ficewa Daga Gaza

Kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi cewa, Isra'ila na da burin kakkabe tare da share Falasdinawa da kuma tilasta musu ficewa daga zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi cewa, Isra'ila na da burin kawar da Falasdinawa da kuma tilasta musu ficewa daga zirin Gaza.

Hamas ta ce: “an gano shahidai kusan 100 bayan da sojojin mamaya na sahyoniyawa masu aikata laifuka suka janye daga unguwannin Al-Rimal da Tal Al-Hawa a cikin birnin Gaza, wadanda akasarinsu sun yi shahada da harsashin bindigar ‘yan mamaya, yana nuni da matakin da ‘yan ta’addar suka bi ta wannan gwamnati da nufin kakkabewa tare da tilastawa mutanenmu yin hijira daga kasarsu,”.

Hamas ta yi kira ga kotun kasa da kasa da ta tattara bayanan ayyukan Isra'ila tare da dorawa kasar alhakinsu.

A wata sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar, ta ce " laifin da sojojin mamaya na 'yan ta'adda suke aikata a unguwar Abu Iskandar da ke arewacin birnin Gaza, da kuma hari kan fararen hula da ba su da kariya, ciki har da yara da mata, a kan tituna, da kuma ci gaba da aikata laifukan sari-ka-noke na farar hula, musamman a kusa da cibiyar kiwon lafiya ta Nasser da ke Khan Yunus, wani ci gaba ne na yakin da ake ci gaba da kawo karshen yakin da makiya yahudawan sahyoniya suke yi kan al'ummar Palastinu a zirin Gaza, a gaban idon duniya baki daya."

"Muna kira ga kotun kasa da kasa, wacce ta amince da wani tsari na kare fararen hula daga ayyukan kisan kiyashi, da ta bi diddigin wadannan laifukan da ake ci gaba da yi tare da rubuta su."

"Muna kuma kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa tare da daukar kwararan matakai don tabbatar da kawo karshen wadannan munanan laifuka."

Da sanyin safiyar Lahadi, an gano gawarwaki kimanin 100 bayan da sojojin Isra'ila suka janye daga wasu unguwanni biyu na birnin Gaza. Yawancin gawarwakin dai an kashe su ne da harsasan bindiga.