Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

12 Faburairu 2024

06:05:53
1436962

An Kaddamar Da Gagarumin Jerin Gwano Domin Tunawa Da Cika Shekaru 45 Da Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci A Dukkanin Garuruwan Kasar Iran.

An fara gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru arba'in da biyar da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a tun mako guda da ya wuce in da aka karkare da manyan taruka a jiya yau Lahadi a Tehran babban birnin kasar Iran da dukkan lardunan kasar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an kaddamar da tattakin tunawa da cika shekaru arba'in da biyar da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Tehran babban birnin kasar Iran da dukkanin lardunan kasar.

A safiyar jiya Lahadi ne aka fara gudanar da jerin gwano na tunawa da cika shekaru arba'in da biyar da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Tehran babban birnin kasar Iran da dukkanin lardunan kasar, inda ake gudanar da jerin gwano a larduna da birane sama da 1,400 da kauyuka dubu 35 na kasar.

An fara gudanar da shagulgulan ne a dandalin Azadi da ke birnin Tehran, tare da rera taken kasa da kade-kade da wake-wake da tsalle-tsalle na gargajiya, da jirage masu saukar ungulu na watsa furanni ga mahalarta taron.

Inda aka kammala tattakin tare da fitar da sanarwar karshe da kuma jawabin shugaban kasar Iran Ayatullah Ebrahim Raisi a dandalin Azadi da ke babban birnin Tehran.

Kafofin yada labarai na kasashen waje da na cikin gida suna bayar da rahotannin bukukuwan ta hanyar wakilansu da masu daukar hoto da ke birnin Tehran, wadanda yawansu ya kai fiye da 7,300 na Iran da na kasashen waje da kuma 'yan jarida.