Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

12 Faburairu 2024

04:40:14
1436921

An Kashe Sojojin Yahudawan Sahyoniya 11 A Wani Kazamin Harin Kwantan Bauna Da Aka Kai A Kudancin Gaza

Sojojin yahudawan sahyoniya 11 ne aka kashe a wani kwanton bauna da dakarun gwagwarmayar Palasdinawa suka yi.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA -  ya bayar da rahoton cewa, an kashe sojojin yahudawan sahyoniya 11 da suka hada da jami'ai da dama a wani harin kwantan bauna da dakarun gwagwarmayar Palastinawa suka yi a garin Khan Yunus da ke kudancin Gaza.

Shafin sadarwar tashar talabijin ta Sahayoniya ta bayar da rahoton cewa, sojojin wannan gwamnati na cikin mawuyacin hali a birnin Khan Yunus.

A cewar rahoton, sojojin sun auka cikin wani mummunan kwanton bauna don haka halin da sojojin ke ciki yayi tsamari sosai.

Kafofin yada labaran yahudawan sun kara da cewa mika gawarwakin sojojin da suka mutu da wadanda suka jikkata ya dauki sa'o'i da dama bayan harin kwantan bauna da kungiyar Hamas ta kai.

Majiyoyin yahudawan sahyoniya da ba na hukuma ba sun ruwaito cewa, Daniel Hagari, kakakin sojojin wannan gwamnatin, zai gabatar da wani labari mara dadi game da wani abu da ya faru a Khan Yunis da karfe 6 na safe agogon kasar.

Wadannan munanan hare-hare an kaiwa sojojin yahudawan sahyoniyawan ne ahalain da suke kan hanyar kai hari ta kasa a Rafah. Harin da ya gamu da kakkausan martani daga wajen al'ummar duniya kuma kasashe da dama sun bukaci a dakatar da gwamnatin sahyoniyawan da ke kai hari a Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Rafah, iyakar kudancin Gaza da Masar, shi ne yanki daya tilo da har yanzu ba a kai wa hare-haren kasa da gwamnatin sahyoniyawa ke kaiwa ba, wanda kuma ake daukarsa a matsayin mafaka ga fiye da rabin al'ummar Gaza miliyan 2.3.

Tuni dai firaministan gwamnatin yahudawan sahyoniya Benjamin Netanyahu ya sanar da kai harin na kusa da birnin Rafah inda ya ce ya bukaci sojojin wannan gwamnati da su shirya tsaf domin kwashe dubban daruruwan mutane daga wannan yanki.