Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

8 Faburairu 2024

16:09:11
1436254

ABNA Na Taya Al'ummar Musulmi Murnar Zagayowar Ranar Da Aka Aiko Manzon Rahama(Sawa) 27/Rajab 13 Kafin Hijrah

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Hakika an aiko ni domin na cika kyawawan halaye"

A irin wannan rana ne Allah ta’ala yaiwa Al’ummar duniya gaba daya tagomashi na Aiko masu da Annabin Rahama cika makon Annabawa Shugaban Manzanni Annabi Muhammad SAWA hakan ya faru a lokacin da Manzon Rahama yabkai shekaru 40 na Rayuwarsa Mala’ika Jibrail As yazo masa da sakon Ubangiji na Busharar kasancewarsa Annabi Manzon wannan Al’umma lokacin yana Kogon Hira inda ya karanta masa farkon Ayoyi Biyar na Surar Alak bayan ya saurare wanann bushara ya koma zuwa gida yana me dauke nauyin wannan sako ya kwanta akan shinfidarsa sai Mala’ika ya sake sauka da wahayi na Biyu na Ayoyi uku na surar Mudassir sai Annabi ya tashi ya fara Aikin kira zuwa ga Allah wanda ya fara kira kuwa ta kasance matarsa Sayyidah Khadijah Da dan Baffan sa Imam Ali As. Sannan bawansa Zaidu dan Harisa wadannan sune suka fara Imani da Annabin a matakin farko na wannan Kira. 

Bayan haka, Manzon Allah (SAW) ya ci gaba da Sallah a farfajiyar dakin Allah, sai Khadijah (a.s) da Ali (a.s) suka bi shi suna masu yin koyi da yi shi.

Wadannan mutane uku sun reni tare yada Musulunci da rayukansu da dukiyoyinsu.

Bayan haka Annabi yakan kira na kusa dashi a da abokansa daya bayan daya lokacin bai kira mutane gaba daya ba har sai da sakon yazo yana mai cewa: وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ alokacin ne kiransa a bayyane ya fara.

A ra'ayin 'yan Shi'a, manzancin Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ne a ranar 27 ga watan Rajab shekara ta 40 ta shekara ta Fil kuma yana da shekaru 40 a duniya. Eid Mab'ath daya ne daga cikin manyan bukukuwan Musulmi.

Manufa da anfanin aiko Manzo

Yazo a cikin Alkur’ani mai girma da hadisai na Musulunci, musamman a cikin Nahjul Balagha, akwai kalmomi da dama da suka shafi hadafi da aiko manzancin Manzon Allah (saww), wasu daga cikinsu akwai kamar haka:

1- Alkur'ani mai girma: "Ya kai Annabi mun aiko ka kana mai shaida, kuma mai bushara, matsayin Annabi mai kira zuwa ga Allah da izininsa, kuma fita mai haskakawa".

2- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Hakika an aiko ni domin na cika kyawawan halaye"..


Matakan aiko Manzon Allah Sawa

1- A mataki na farko, Allah ya umarci Manzon Allah (SAW) da ya kira mutane wadanda suk fi tabbatuwa a hankali da ruhi zuwa Musulunci. Wannan kira da ba na gaba ki dayan jama'a ba ya dau tsawon shekaru uku.

2- A mataki na biyu Manzon Allah (S.A.W) ya fara kiran al'umma a bayyane kuma sanu a hankali kiransa ya yadu a tsakanin jama'a.

Mushrikai Don fuskantar Musulunci, da farko sun riki tsarin yaudarar kwadaitarwa ga Manzon Allah (SAW) sannan suka fara yi masa tsarin barazana.

Bayan gazawar da rashin nasara da suka sha wajen fuskantar Kur'ani, kuraishawa sun yi kokarin gabatar da Alkur'ani a matsayin tatsuniyoyi na farko da kuma maganar Annabi (SAW) a matsayin sihiri.


3- A mataki na uku tsarin kuraishawa shi ne su je wurin wadanda suka fi kowa ilimi da neman su yi la’akari da batutuwa masu sarkakiya tare da keɓantattun amsoshi sannan su gabatar da su a gaban Manzon Allah (SAW) don ya ba su amsa. Idan ya kasa ya zamo matsayinsa ya fadi a idon jama'a. Don haka ne suka je wajen Yahudawan Yathrib, amma Manzon Allah (SAW) ya amsa dukkan tambayoyinsu da wahayi.

Bayan rashin nasara a jere, shugabannin kuraishawa sun cimma matsayar cewa hanya daya tilo ta tinkarar Musulunci ita ce a yi amfani da tashin hankali da azabtarwa don sanya tsoro da firgici a cikin zukatan musulmi da hana masu kishin Musulunci shiga wannan addini.

Bayan sun sha kaye a jere, shugabannin Makkah sun cimma matsaya kan cewa su gabatar da shawarwari na lumana ga Manzon Allah (SAW) don hana ci gaban Musulunci, amma Allah Madaukakin Sarki ya bayyanar da mugun nufi da suke nema da saukar surar Kafirun ya na mai basu kakkausar amsa mai tsauri. Karshe dai kiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasaallam ya yi nasara bayan shan wahalhalu da yakoki masu yawa.