Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

8 Faburairu 2024

11:49:59
1436162

Jagoran: Tsarin Duniya Na Yanzu Lalataccen Tsari Ne

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Lokacin Da Yake Ganawa Da Jami'ai Da Wakilan Gwamnati Da Jakadun Kasashen Waje: Musibar Gaza Bala'i Ga Duniyar Musulunci Kai Sama Da Haka Ma Musiba Ce Ta Bil'adama, Kuma Hakan Yana Nuni Da Cewa Tsarin Duniya A Yau Lalataccen Tsari Ne Na Kuma Ba Mai Dorewa Ba Ne.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Lokacin Da Yake Ganawa Da Jami'ai Da Wakilan Gwamnati Da Jakadun Kasashen Waje: Musibar Gaza Bala'i Ga Duniyar Musulunci Kai Sama Da Haka Ma Musiba Ce Ta Bil'adama, Kuma Hakan Yana Nuni Da Cewa Tsarin Duniya A Yau Lalataccen Tsari Ne Na  Kuma Ba Mai Dorewa Ba Ne. Ma'ana A Yau Wani Muhimmin  Sashe Na Masu Ikon Mulki Duniya Suna Goyon Bayan Ayyukan Tsarin Mulkin Yahudawan Sahyoniya Masu Laifi Da Suka Bata Hannayensu Da Jinane, Wanda Ya Zamo Ɓangaren Da Suke Yaƙa Ba Mayaka Ba Ne, Illa Yara Da Mata Da Marasa Lafiya Da Asibitoci Da Gidajen Mutane.Amurka Da Ingila Suke Mara Masu Baya, Da Yawa Daga Kasashen Turawa Suna Goyon Bayansu, Da Ma Ƙasashen Da Suke Masu Biyayya Suma Sunan Mara Masu, Zamu Iya Fahimtar Lalacewar Tsarin Mulkin Duniya Daga Abinda Ke Faruwa A Gazza, Kuma Wannan Tsarin Bazai Dawwama Ba, Ba Zai Ci Gaba Ba, Zai Wargaje.