Kamfanin dillancin labaran
Ahlul-Baiti (AS) – ABNA-ya habarta cewa: a daren jiya Talata ne majiyoyin yada
labarai suka sanar da cewa, “Rizk Al-Gharabili” dan jarida kuma manajan wata kafar
yada labaran Falasdinu ya yi shahada a hare-haren da makiya yahudawan sahyoniya
suka kai a Gaza.
Al-Gharabili shi ne darektan cibiyar yada labaran Falasdinu, wanda ya yi shahada a harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai wa Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.
Bisa shahadar wannan dan jarida, adadin wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa mutane 123 tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoba.
Idan dai ba a manta ba ma'aikatar lafiya ta Falasdinu mai hedkwata a Gaza ta sanar da cewa tun daga ranar 7 ga watan Oktoba a daidai lokacin da aka fara yakin guguwar Al-Aqsa, Palasdinawa 27,585 ne suka yi shahada a Gaza yayin da wasu 66,978 suka samu raunuka.
Har ila yau ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da samun karuwar shahidai da jikkatar wasu a yankin Zirin Gaza sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahyuniya suke yi.