Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

7 Faburairu 2024

04:32:12
1435872

Harin Da Isra'ila Ta Kai Kan Wani Masallaci A Gaza: Shafukan Al-Qur'ani Sun Jike Da Jinin Wadanda Aka Kashe + Bidiyo

Kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu ya wallafa hotuna da ke nuna yadda mutane ke kwashe baraguzan masallacin da aka lalata a baya bayan nan a harin da Isra'ila ta kai a Deir al-Balah. Hotunan sun kuma nuna tarin litattafan addini, da litattafan addu'o'i da yagaggun kwafin kur'ani mai jike da jini.

A cewar kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - Shafukan kur'ani suna jike da jinin wadanda abin ya rutsa da su da ke zaune acikin masallacin suke ibada, wannan shi ne abin da ya rage daga harin bam da Isra'ila ta kai a Deir al-Balah a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu ya wallafa hotuna da ke nuna yadda mutane ke kwashe baraguzan masallacin da aka lalata kwanan nan a harin da Isra'ila ta kai a Deir al-Balah.

   Hotunan sun kuma nuna tarin litattafan addini, da litattafan addu'o'i da yagaggun kwafin kur'ani mai jike da jini.

A ranar Lahadin da ta gabata ce gwamnatin sahyoniyawan ta kai hari a wasu gidaje biyu da wani masallaci a tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe mutane 29 tare da jikkata wasu akalla 60 na daban.

Wasu hare-hare ta sama da aka kai a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, ya yi sanadin shahadar kananan yara biyu.

Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar, yakin Gaza ya lakume rayukan mutane kusan 27,365, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 66,630, kuma sama da mutane 8,000 ne ke karkashin baraguzan ginin.

Fiye da rabin al'ummar Zirin Gaza sun yi hijira zuwa kudancin birnin Rafah, inda dubban daruruwansu ke zama a cikin tanti na wucin gadi ko kuma a fili falalin kasa.

   Hakazalika Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza a cikin 'yan makonnin nan.