Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

6 Faburairu 2024

08:58:47
1435656

ABNA Na Ta Ya Al’ummar Musulmi Ta’aziyyar Shahadar Imam Musal Kazim As 25/Rajab/ 183h

A Irin Wannan Rana Ne Dai Shahadar Imam Musal Kazim As Takasance A Shekarata 183h A Birni Bagdaza

              Imam musa As dan Imamu Ja’afar Assadik As wanda akewa lakabi da Alkazim ana masa Alkunya da Abul Hasan da Abu Ibrahim Shine Imam na Bakwai cikin Jerin A’immah da Manzon Rahama ya barmana, mahaifiyar ana ce da ita Humaidah yar Saa’id mutuniyar Afrika.

An haifeshi a wani waje dake tsakain makka da madinah da ake kira da Abwa’a a ranar 7/safar shekara ta 168h ya rayu shekaru 55 ya kuma dauki shekaru 35 yana mai rike da Mas’uliyyar Imamah

Imam ya rayu bisa kulawa da tarbiyyar  mahaifinsa Imam Ja’afarussadik wanda tun yana karami alamomi na kwazo da hazaka da ilimi littafan tarihi sun kawo labarin wata tambaya da Abu Hanifah yayi masa alokacin da yana karami inda yace masa: Daga wa Sabo yake Gangarowa?

Sai ya bashi amsa da cewa: Lalla babu makawa sabo yana ganganrowa ne daga Bawa ko ubangijinsa ko kuma daga garesu su biyun.  Idan ta kasance daga ubangiji to shi mai adalci ne kuma yafi kowa yin adalci bazai zalunci bawansa da kama sa da abinda bai aikata shi ba, idan kuma daga garesu su biyun take to ta kaga yayi tarayya dashi akai to kaga wanda yafi karfi da daukaka shine yafi cancanta da yafiya ga rarrauna wato bawansa, idan kuma daga bawa ne sabon ya gangaro to kaga kansa lamarin ya fada.  Kuma kaga shi bawa an hanashi aikata sabo kaga shi ya cancanci abashi ladar aikin kirki da dana zunibi kuma akanshi shiga wuta da Aljanna yake tabbata.  

Imam ya fara gudanar da ragamar Imamancinsa bayan shahadar mahaifinsa Imam Ja’afar As a shekarata 148h a karshen lokacin kalifancin Mansur Abbasy wanda Imam yayi zamani da kalifofin da suka zo bayan Mansur wato Almahdi, Alhady, da Harunar Rashid. Wanda a lokacinsa aka shahadantar da shi bisa umarnin khalifah Harunar Rashid La.

Lokacin rayuwar Imam As ya dace da lokacin da daular Abbbasawa take da karfinta na Zalunci da muzgunawa Al’umma wanda Imam ya dauki matakin yin takiyya a ayyukokinsa kuma ya umarci mabiyansa da yin hakan saboda su kasance cikin aminci inda bai yadda ya kasance cikin masu yin zangazanga na yan shi’a data rinka faruwa a lokacinsa inda yayi kokarin assasa wakilai a garuruwa da dama domin su wakilce shi da kuma samun saukin sadarwa a tsakaninsu, har wala yau kuma lokacinsa ya dace da bayyanar kungiyoyi da dama na shi’a kamar Ismailiyya, Fadahiyya, Nawusiyya bayan shahadarsa kuma kungiyar Wakifiyyah ta bayyanah.

Anyi wa imam lakabi da Kazim ne saboda hadiye fushin da yake dashi inda littafn tarihi suka shaida da yawan Iliminsa da ibadarsa da kyautarsa da hakurinsa.

An kama Imam sau biyu bayan tuhime-tuhume da makiyansa suka kai wajen khalifa Haruna inda ya sanshi cikin kurkun Isah dan Ja’afar dake Basara bayan an taho dashi daga Madina bayan wani lokaci kuma aka maida shi kurkukun Fadl dan Rabi’i dake Bagdag sannan aka maida shi na  Fadli dan Yahaya sannan kurkukun Sinde dan Shahik wanda acikinsa yayi shahada salamullahi Alaihi.  

Imam yayi shahada a ranar 25 ga watan Rajab a Birnin Bagdaz shekara ta 183h kabarin Imam yana yankin Kazimiyyah dake Iraki wanda a wannan ranar da ake tunawa da shahadarsa an kaiwa masu zuwa ziyararsa hari wato a ranar talata 25/Rajab shekara ta 1442h.