Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

5 Faburairu 2024

07:26:11
1435323

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Gana Da Rukunin Kwamandojin Sojojin Sama Da Dakarun Tsaron Saman Iran

Taron rukuni na kwamandojin sojojin sama da na tsaron sama na sojoji tare da jagoran juyin juya halin Musulunci ya gudana ne a yau Litinin 05/02/2024

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta cewa:  a safiyar yau Litinin 05/02/2024 wanda yayi daidai da 16/11/1402Shamsi A daidai lokacin munasabar raneku goma na alfijirin jajibirin zagayowar ranar mubaya'ar tarihi mai cike da tarihi da gungun musulmi suka yi wa Imam Khumaini (RA) a ranar 19 Bahman 1357, gungun kwamandoji da ma'aikatan sojojin sama da na rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci Iran sun gana da jagoran juyin juya halin Musulunci.