Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBait (ABNA)
ya habarta cewa: matsugunan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ba su
kariya, sun kai hari a wata rumfar raguna ta Falasdinawa a yankin Arab
al-Malihat da ke arewacin birnin Jericho tare da sace wasu daga cikin
dabbobinsu. Kamfanin dillancin labaran tashar Aljazeera ya fitar tare da buga
hotunan wasu yahudawan sahyuniya wadanda suka kai farmaki a kauyen Ras al-Awja
dake arewacin birnin Jericho da ke gabar yammacin kogin Jordan da karfin tsiya
tare da goyon bayan sojojin yahudawan sahyuniya inda suka sace tare da kwace wasu
tumaki daga hannun Falasdinawa
Madogara : ابنا
Lahadi
4 Faburairu 2024
07:43:26
1435030
Bidiyo Yadda Isra'ilawa Ke Satar tumakin Falasdinawa