Kamfanin Dillancin Labarai na
AhlulBait (ABNA): Ministan Awkaf na Masar ya ce an rufe Masallacin Sayyida
Zainab As da ke birnin Alkahira na wani dan lokaci domin a gaggauta aikin gyara
da sabunta shi.
Muhammed Mukhtar Gomaa ya fada a wani sakon da ya wallafa a shafin X, wanda a da ake kira Twitter, cewa aikin gyare-gyaren yana kan mataki na karshe.
Ya ce rufe masallacin na wucin gadi ya zama dole domin dan kwangilar ya gaggauta gudanar da gyare-gyaren karshe.
An rufe masallacin ne a ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairu, kuma ana sa ran bude masallacin kafin a shiga watan Ramadan mai alfarma, in ji shi.
Masallacin Sayyida Zainab As wani masallaci ne mai cike da tarihi a babban birnin kasar Masar. Ya kasance daya daga cikin manya-manyan masallatai kuma mafi girma a tarihin kasar. Kamar yadda wasu bayanai suka nuna, masallacin anan wurin aka binne Sayyida Zainab (SA).
Ya kasance babban wurin gudanar da ayyukan kur'ani da addini a cikin birnin tsawon shekaru aru-aru. Ma'aikatar Awkaf ta aiwatar da aikin gyara na karshe a masallacin a shekarar 1969.