Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

4 Faburairu 2024

05:36:41
1434991

Musulman Shi'a Sun Halarci Sallar Juma'a a Cibiyar Musulunci da ke birnin Hamburg na Jamus

Mabiya mazhabar Shi'a mazauna birnin Hamburg sun halarci sallar Juma'a, wanda aka gudanar a cibiyar Musulunci da ke wannan birni.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA ya habarta cewa: an gudanar da sallar juma'a a birnin Hamburg na kasar Jamus, inda musulmin shi'a suka halarta.Mabiya Shi'a mazauna birnin Hamburg sun halarci sallar Juma'a, wanda aka gudanar a cibiyar Musulunci da ke wannan birni.

Hujjat al-Islam wal-Muslimeen Sheikh Dr. Muhammad Hadi Muftah daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya jagoranci sallar Juma'a tare da gabatar da hudubobin Juma'a guda biyu ga wadanda suka halarta.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ayatullah Sheikh Reza Ramadani ne yake jagorantar sallar Juma'a a wannan cibiya ta Musulunci.

Masu shirya wannan cibiya ta addinin musulunci a birnin Hamburg na kasar Jamus suna gudanar da ayyuka da dama a lokuta daban-daban na addini da al'adu da suka hada da gudanar da bukukuwan maulidi da kuma gudanar da majalisai na Husaini As a ranakun Muharram da sauran abubuwan addini da suka faru.