Kamfanin dillancin labaran
Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA ya habarta cewa: A farkon yakin da yahudawan
sahyoniyawan suke yi da kungiyar Hamas, sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya
sun ayyana Rafah a matsayin wani yanki mai tsaro, amma a karshe dai ta sha
fuskantar hare-hare ta sama daga wannan gwamnati.
Daya daga cikin Falasdinawa mazauna wannan yanki ya ce: Mun zo Rafah ne kamar yadda Isra'ilawa suka ce. Sun ce wannan yanki yana da lafiya da aminci. Amma yanzu an sake yi mana barazana.
Wani Bafalasdine da ke zaune a Rafah ya ce: Mun dauka cewa Rafah ita ce mafakarmu ta karshe. Amma kuma sojojin za su shiga Rafah kamar yadda suka kai hari a wasu sassan Gaza. Babu wani wuri mai aminci a nan.