Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

2 Faburairu 2024

20:28:32
1434610

Sheikh Naim Qasim: Wajibi Ne Dukkan Larabawa Da Musulmi Su Goyi Bayan Gaza

Mutane da yawa sun zarge mu saboda mun goyi bayan Gaza! Mun ce dole ne mu goyi bayan Gaza kuma ku ma dole ne ku goyi bayan Gaza, dukkan Larabawa da musulmi gaba daya dole ne su goyi bayan Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Sheikh Naim Qassem babban shugaban kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon yayin da yake bayani ya ce: Mutane da yawa sun zarge mu saboda mun goyi bayan Gaza! Mun ce dole ne mu goyi bayan Gaza kuma ku ma dole ne ku goyi bayan Gaza, dukkan Larabawa da musulmi gaba daya dole ne su goyi bayan Gaza.

Muna tambayar su, me ya sa ba ku goyon bayan Gaza? Me ya sa ba za ku tsaya mata ba? Me ya sa ba ku yanke alaka da Isra'ila ba? Muna tambayar ku, me ya sa ba ku goyon bayan Falasdinu? Ku ko wani ba ya da hakkin ya tambaye mu dalilin da ya sa muke goyon bayan Falasdinu, domin hakkinmu ne, hakkin Palasdinu, hakkin al-Aqsa da kuma hakkin dan Adam ne.