Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

1 Faburairu 2024

11:48:07
1434307

Cikakken Rahoton Bukin Bude Sabbin Kafofin "Wiki Turath" Da "Shia Data" + Hotuna Da Bidiyo

An gudanar da bikin bude wasu sabbin ayyuka guda biyu na Wiki na Shi'a mai taken "Wiki turath" da "Shi'a Data" a birnin Qum tare da karanta sakon Ayatullah Makarim Shirazi da kuma jawabin Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a jajibirin cika shekaru 45 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran, an bude wasu sabbin ayyuka guda biyu na kundin tarihin Shi'a na Wiki mai taken "Wiki turath" da " Shi’a Data” an gudanar da shi ne da azahar din ranar jiya Laraba – 11 ga Bahman 1402 – wanda yayi daidai da 31 ga watan Yunairu 2024 tare da gudanar da matanin sakon Ayatullahi Makarem Shirazi a zauren taron Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya da ke birnin Qum.

Nassin sakon Ayatullahi Makarim Shirazi yazo kamar haka:

“Da farko muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa kokarin masu tsarawa da masu fada aji da masana da kuma wadanda abin ya shafa ya kai ga cimma matsaya da kuma sanya damar yin amfani da shirye-shirye guda biyu masu fa’ida wajen buga koyarwar Ahlul-Baiti (a.s) domin saukakawa da gabatarwa masu sha'awar sanin Ilimomin Musulunci da koyarwar ruhi.

Tattara tare da ingantawa da yaɗawa da samar da hanyoyin samun koyarwar mazhabar shi'a da kuma abubuwan tarihi na maluman musulmi tare da tattara bayanai da tantance abubuwan da suke da su da sauran kokari masu fa'ida da aka gudanar a cikin wadannan shirye-shirye guda biyu, in Allah Ya yarda, zasu zamo share fagen hanyoyin da dalilai na ci gaba a cikin bincike a cikin koyarwar Musulunci da littafai Malaman Shi'a da ingantaccen kuma cikakkiyar sanin aqidar shi'a ta Imamiyyah za a nuna su ga duk mai neman gaskiya.

A duniya ta yau, inda ake yin gasa wajen saurin isar da bayanai, tantancewa da inganci. kuma makiya suna kokarin karkatar da fuskar gaskiya da jawo hankulan mutane zuwa ga tafarkin karya, wajibi ne mu yi kokari da gaske wajen karfafa gwiwa wajen bayanin mu a cikin sararin samaniya kafofin yanar gizo, wanda zai zamo yunkurin da zai gaskata wannan misali ne na:

 "«وَ أَعِدُّوا لَهُمْ مَا اسْتَطَعْتُمْ مِنْ قُوَّة»

A wannan bangaren, ina mika godiyata da jinjinata ga dukkan jami'ai da masu ruwa da tsaki, da masu bincike da masu shirya shirye-shirye da suka taka rawa a cikin wadannan manyan ayyuka guda biyu, kuma ina yi musu fatan Allah ya ba su nasara.