"Michael Fakhri",
wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan abinci, ya ce: "Yunwa a Gaza
ta zama babu makawa bayan da wasu kasashe suka dakatar da taimakon kudi ga
Hukumar ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA).
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA ya habarta cewa: Fakhri ya kara da cewa a wani taron manema labarai da ya kira dakatar da tallafawa UNRWA na nufin barin Falasdinawa miliyan 2.2 a zirin Gaza cikin matsananciyar yunwa.