Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

28 Janairu 2024

06:37:03
1433032

MSF: Babbar Cibiyar Lafiya Ta Gaza Ta Ruguje A Cikin Hare-Haren Isra'ila

Manyan kungiyoyin kiwon lafiya sun buga kararrawa kan rugujewar muhimman ayyukan kiwon lafiya a cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza, a daidai lokacin da Isra'ila ke kai hare-hare ba kakkautawa a Khan Yunis da ke kudancin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - Abna ya habarta cewa: Manyan kungiyoyin kiwon lafiya sun yi kararrawa kan rugujewar muhimman ayyukan kiwon lafiya a cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza, a daidai lokacin da Isra'ila ke kai hare-hare ba kakkautawa a Khan Yunis da ke kudancin Gaza.

Kungiyar agaji ta likitocin, wacce aka fi sani da MSF a Faransa, ta fada a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa ayyuka a asibitin Nasir sun durkushe, wanda hakan ya bar mutane ba su da zabin zuwa neman magani.

Ta ce akasarin ma’aikatan asibitin Nasir, tare da dubban ‘yan gudun hijirar da ke matsuguni a cikin ginin, sun yi gudun hijira ne a kwanakin da suka biyo bayan umarnin korar da sojojin Isra’ila su kai ne.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, MSF ta ce "ikon aikin tiyatar asibitin ya kusan zama babu shi kwata-kwata, kuma kadan daga cikin ma'aikatan lafiya da suka rage a asibitin dole ne suna fama da karancin kayayyaki da ba su isa don gudanar da al'amuran kuma basu wadatar tare da dacewa da yanayin rayuka da dama ke ciki ba".

MSF ta ce akalla majiyyaci daya a asibitin ya mutu ranar Laraba saboda babu wani likitan tiyatar kashi.

"Tsakanin majiyyata 300 zuwa 350 na ci gaba da zama a Asibitin Nasir, ba za su iya ficewa ba saboda yana da matukar hadari kuma babu motocin daukar marasa lafiya."

Jami'in kula da lafiya na MSF a Falasdinu Guillemette Thomas ya ce Asibitin Nasir da Asibitin Gaza na Turai "ba za a iya kaiwa garesu ba" kuma babu wani tsarin kula da lafiya a Gaza da yayi saura.

“Wadannan tsararrun hare-hare da ake gudanrwa akan harkokin kiwon lafiya ba za a amince da su ba kuma dole ne a kawo karshensu yanzu domin wadanda suka jikkata su samu kulawar da suke bukata. Dukkanin tsarukan kiwon lafiya sun kasance marasa aiki, ”in ji Thomas.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya fada a ranar Juma’a cewa ana ci gaba da gwabza fada a kusa da asibitin kuma cibiyar “ta rasa mai, abinci da kayayyaki.”

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a kan X. "Muna neman tsagaita bude wuta nan da nan domin mu iya sabunta kayayyakin ceton rai da gaggawa."

Isra'ila ta fara yakin kisan kare dangi a Gaza bayan da kungiyar Hamas ta kai mata hari a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Akalla Falasdinawa 26,083 ya zuwa yanzu aka kashe, yayin da 64,487 suka jikkata a Gaza, yawancinsu mata da kananan yara ne, a cewar sabon alkalumman da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar.

Sai dai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kashe Falasdinawa 183 tare da jikkata 377.