Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

27 Janairu 2024

10:31:02
1432782

Martanin Jigajigan Yahudawan Sahyoniya Kan Hukuncin Kotun Duniya:

Bin Ghafir: "Kotun Hague abin kunya ce" bai kamata kotun Hague ta ya yarda ta saurari tare da yanke hukunci da zai zamo illa ga ci gaba da wanzuwar gwamnatin Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: bayan hukun da kotun kasa da kasa ta yanke dangane da karar da kasar Afirka ta kudu ta kai gaban wannan kotun manyan shugabannin gwammanin yahudawan sahayuniya sun maida martani daya bayan daya danagane da wannan hukunci inda su kai Allah wadai da shi zamu fara kawo maku wadanna martanoni kamar haka:

 "Benjamin Netanyahu", firaministan gwamnatin mamaya na Isra'ila, ya dauki matakin da kotun duniya da ta dauka na gudanar da bincike kan laifukan kisan kare dangi na wannan gwamnati a Gaza a matsayin mummunan tabo da ba zai taba gogewa ba.

Yoav Gallant ministan yakin gwamnatin sahyoniyawan a cikin wata sanarwa da ya fitar da ke kalubalantar kotun kasa da kasa ya ce: Kotun duniya ta wuce aikinta bayan da ta amince da bukatar Afirka ta Kudu ta tattauna batun kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza kuma gashi har batai watsi da korafin gaba daya ba.

Shima Bin Ghafir, ministan tsaron cikin gida na gwamnatin sahyoniyawan, ya yi kira da a ci gaba da yakin da wannan gwamnatin take yi akan mazauna zirin Gaza, yana mai da'awar cewa "Kotun Hague abin kunya ce", yana mai cewa: bai kamata kotun Hague ta ya yarda ta saurari tare da yanke hukunci da zai zamo illa ga ci gaba da wanzuwar gwamnatin Isra'ila.

Shi ma Bezalel Smotrich, ministan kudi na gwamnatin sahyoniyawan, ya zargi alkalan kotun kasa da kasa da ke birnin Hague da nuna goyon baya ga mazauna Gaza, ya kuma bukaci kasashen duniya da su bude kofofinsu na karbar mazaunan Gaza, batun da yake bayyana niyyar da kuma kokarin matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na mamaye zirin Gaza tare da korar mazaunanta daga gidajensu.

  "Dani Danon", mamba na Knesset (Majalisar dokokin Sahayoniya) shi ma ya bayyana hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke kan gwamnatin sahyoniyawan a matsayin abin ban dariya kuma gaba daya ya sabawa hakikanin gaskiya da yake a kasa sannan ya ce: "Wannan goyon bayan hukuncin ba zai kawar da mu daga cimma burinmu ba, wato ruguza Hamas da 'yanto wadanda akai garkuwa da su ba na fursunonin Isra'ila.