Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

27 Janairu 2024

05:36:15
1432682

Wace Ce Alƙaliyar Kotun Hague Da Ta Ke Goyon Bayan Isra'ila?!

ai shari'a Julia Sebutinde, 'yar kasar Uganda ce mai shari'a wadda ta yi wa'adi na biyu a kotun kasa da kasa bayan sake zabenta a ranar 12 ga Nuwamba, 2020. Wacce ita ce kuma shugaban jami'ar Royal Muteesa ta Masarautar Uganda a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Julia Sibutinde ita ce alkaliya daya tilo a kotun duniya da ta ci gaba da kada kuri'ar amincewa da gwamnatin sahyoniyawan a shari'ar da ake yi a Afirka ta Kudu dangane da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza.

Julia Sibutinde ita ce alkaliya daya tilo a kotun kasa da kasa da ta kada kuri'ar amincewa da gwamnatin sahyoniyawa.

Alkalin kotun Isra’ila na kotun kasa da kasa ya kada kuria’ar har sau biyu a kan Isra’ila, amma hukuncin Julia Sibutinde ta goyi bayan Isra’ila a dukkan shari’o’i shida.

Mai shari'a Julia Sebutinde, 'yar kasar Uganda ce mai shari'a wadda ta yi wa'adi na biyu a kotun kasa da kasa bayan sake zabenta a ranar 12 ga Nuwamba, 2020. Wacce ita ce kuma shugaban jami'ar Royal Muteesa ta Masarautar Uganda a halin yanzu.

Tun a watan Maris din shekarar 2012 ta kasance alkali a kotun duniya, kuma ita ce mace ta farko a Afirka da ta bayyana a kotun ta duniya.

Kafin a zabe ta a matsayin alkalin kotun kasa da kasa, Sibutinde ta kasance alkali ce a kotun musamman na kasar Saliyo. An nada ta wannan mukamin a shekarar 2007.

Wannan alkaliya ta sha suka sosai saboda hukuncinta na baya-bayan nan da ta yanke a kotun duniya, musamman idan aka yi la'akari da alakar Uganda da gwamnatin Isra'ila.

Uganda da gwamnatin yahudawan sahyoniya suna da huldar diflomasiyya, kuma Uganda ta sha bayyana goyon bayanta ga Tel Aviv a kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa, kuma wannan dangantaka tana kara karfi ta hanyar hadin gwiwa a fannonin tsaro, noma da fasaha.

A zaman da aka yi na yanke hukunci kan matakan wucin gadi da ke da alaka da korafin kisan kiyashi da kasar Afirka ta Kudu ke yi kan gwamnatin sahyoniyawan, kotun kasa da kasa ta bukaci gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ta dauki matakan da suka dace na hana kisan kiyashi a Gaza tare da jaddada cewa ba za ta amince da bukatar Tel Aviv ba na yin watsi da korafin Afirka ta Kudu.