Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

26 Janairu 2024

20:22:46
1432619

Kotun Hague: Dole Ne Isra'ila Ta Daina Kashe-Kashe Da Cutar Da Al'ummar Gaza Tare Da Daukar Matakan Gaggawa Don Biyan Bukatun Jin Kai Na Al'ummar Gaza.

A yau ne kotun kasa da kasa ta fitar da hukuncin farko kan korafin da kasar Afrika ta kudu ta kai kan gwamnatin sahyoniyawa kan aikata kisan kiyashi.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Baiyt As ABNA ya habarta cewa: kotun ta kasa da kasa ta fara karanto hukuncin ta na musamman dangane da korafin da kasar Afrika ta kudu ta kai kan gwamnatin sahyoniyawan na zargin aikata kisan kiyashi a Gaza da kuma bukatar daukar matakai na musamman.

A wannan zaman kotun ta kasa da kasa ta bayyana damuwa game da ci gaba da asarar rayukan al'ummar Gaza.

Shugaban wannan kotun ta kasa da kasa ta jaddada cewa kotun ba za ta iya amincewa da bukatar gwamnatin Isra'ila na kin karba da amincewa da korafin Afirka ta Kudu ba.

Ta yi nuni da cewa: Muna da hurumin fitar da hukunci kan wasu matakai masu ban mamaki dangane da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Isra'ila, sannan kuma kasar Afirka ta Kudu ma tana da hakkin shigar da kara a gabanta, kuma ba za a amince da bukatar Isra'ila na kin amincewa da ita ba.

An sanar a wannan taron kotun cewa: Yanzu ba za mu sanar da ko Isra'ila ta keta wajibcin da ya shafi yarjejeniyar hana kisan kiyashi ko a'a ba. Mu yanzu muke yanke hukunci kan ko kisan kiyashi ya faru ko bai faru ba, amma zamu yanke akan yiwuwar kisan kiyashi.

Har ila yau, wannan kotun ta bayyana cewa: ayyukan soji a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a wannan yanki da kuma gudun hijirar wasu da dama. Harin na Isra'ila ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa kusan 25,000 tare da jikkata wasu 60,000.

Kotun kasa da kasa ta jaddada cewa: Fiye da kashi 93% na mutanen Gaza ba sa samun abinci. Yarjejeniyar hana kisan kiyashi ta kare al'ummar Palasdinu. Al'ummar Palastinu na da 'yancin samun aminci daga laifin kisan kiyashi.

Shugaban wannan kotun kasa da kasa ta kara da cewa: Mun dauki bayanin da UNRWA ta bayar game da tabarbarewar al'amuran jin kai a zirin Gaza da kuma halin da ake ciki a wannan yanki na fuskantar bala'i. Dole ne Isra'ila ta ɗauki matakan da suka dace don hana aikata laifukan kisan kiyashi ga gungun jama’ar ‘yan adam. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa barnar da aka yi wa fararen hula a Gaza ya zama laifin yaki. Dole ne Isra'ila ta tabbatar da cewa dakarunta ba su aikata laifin kisan kiyashi ba, sannan su dauki matakan inganta yanayin jin kai a Gaza.

Har ila yau, wannan kotun ta bayyana cewa: Dole ne dukkan bangarorin da abin ya shafa a Gaza su bi dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma sakin fursunonin nan take ba tare da wani sharadi ba. Dole Ne Isra'ila Ta Daina Kashe-Kashe Da Cutar Da Al'ummar Gaza Tare Da Daukar Matakan Gaggawa Don Biyan Bukatun Jin Kai Na Al'ummar Gaza. Dole ne Isra'ila ta ɗauki matakan da suka dace don hana tunzura jama'a kai tsaye. Dole ne Isra’ila ta dage wajen kauracewa kisa, take hakki da ruguza al’ummar Gaza.

Kotun ta kuma bayyana cewa rahotannin Afirka ta Kudu suna da ma'ana kuma na hankali ne kuma ya kamata a yi la'akari da su.