Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

25 Janairu 2024

19:52:03
1432411

Ayatullah Sheikh Isa Qasim Ya Gana Da Sheikh Ibrahim Zakzaky

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gana da Ayatullah Sheikh Isa Qasim jagoran Harkar Musulunci ta Bahrain a birnin Qum, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi duniyar Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, ya gana da Ayatullah Sheikh Isa Qasim jagoran Harkar Musulunci ta Bahrain a birnin Qum, inda suka tattauna muhimman batutuwan duniyar Musulunci.

A wannan ganawar Shaikh Zakzaky ya yaba da kokarin Ayatullah Sheikh Isa Qasim har ila yau, Ayatullah Sheikh Isa Qasim ya dauki Shaikh Zakzaky a matsayin abin koyi na Jihadi.

A wannan ganawa wanda ya kasance tare da kaskantar da kai da kyawawan dabi'u na masu addini da na juyin juya hali na duniyar Musulunci, cikin girmama, hakan ya sanya an tuna da malamai da shahidan tafarkin Musulunci da kuma masu fada a ji a tarihi, musamman ma Imam Khumaini (RA).

Ganawar Sheikh Zakzaky Da Shugaban Makarantun Hauza 


Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gana da Ayatullah Alireza Arafi, daraktan makarantun hauza na kasar Iran, tare da gungun malamai da masu gudanar da makarantun hauza.

A cikin wannan ganawar an yi la'akari da mabudin nasarar harkar Musulunci da ci gaban al'adu a Najeriya da Afirka a matsayin abin koyi da Imam Khumaini (RA) da kuma juyin juya halin Musulunci na Iran, ya kuma bayyana cewa: Kafin juyin juya halin Musulunci, ba a samu wani bin mazhabar Shi'a ko guda daya tilo a Nigeria ba, kuma albarkacin shiriyar Imam Khumaini (RA) da kuma albarkar Sayyid Hujjatullah (AS) miliyoyin 'yan Shi'a na rayuwa a Afrika a yau.

Shaikh Zakzaky ya ce: Kimanin shekaru 40 da suka gabata na samu damar zuwa kasar Iran a bikin cika shekara daya da nasarar juyin juya halin Musulunci. Imam Khumaini (RA) ya ba ni Alkur’ani ya ce in je in Kira al’ummar Nijeriya zuwa ga Musulunci da wannan Alkur’ani.

Ya ci gaba da cewa: A yau ana gudanar da tarukan kur'ani da Ahlulbaiti (a.s) tare da halartar dubban mutane, kuma a kowace rana adadin mabiya Ahlulbaiti (a.s) da mabiya Shi'a na karuwa.

A cikin wannan ganawar, daraktan makarantun hauza na kasar Iran, ya yaba da kokari da jajircewar Sheikh Zakzaky na yada al’adu da karantarwar Musulunci tsantsa da kuma jawaban al’adun juyin juya halin Musulunci a Nijeriya, tare da yi masa fatan lafiya da nasara, tare da bayyana fatansa cewa gwamnatin Nijeriya za ta ba da hadin kai da ya dace, ya kuma mika gaisuwa ga ruhin shahidan Musulunci, na gwagwarmayar Musulunci, Gaza, da Nijeriya, musamman tsarkakan ruhin shahidai da Iyalansu.

A ranar Litinin din makon nan ne Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi tafiya zuwa birnin Qum, inda ya ziyarci hubbaren Sayyida Fatima Masoumeh (AS).

..........