Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

25 Janairu 2024

19:32:29
1432406

Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Aka Gudanar Da Khamtamar Mauludin Imam Ali A's A Abuja

Harkar musulunci ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta gudanar kayataccen Mauludi na Wasiyin Manzon Allah (SAWW) wato Imam Ali Dan Abi Dalib (AS) a Merit House dake Maitama Abuja, birnin Tarayyar Nijeriya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Taron wanda aka dauki tsawon kwanaki uku ana gudanar dashi, wanda a ranar farko aka gudanar da Ziyara zuwa Asibiti tare da bada gudummuwar Jini, a ranar ta biyu kuma aka gudanar da wasanni daban-daban na matasa sannan da dare aka gudanar da Majalisi na Imam Ali (AS) inda a yau ake gudanar katama na taron Mauludin.

Taron na yau wanda aka fara shi a yammacin yau wanda aka fara da bude taron da Addu'a sannan karatun Al-Qur'ani mai girma da Ziyara Imam Ali Amiral-Mumineen (AS), sannan aka gudanar da Display daga Intizar da Shotakan Imam Ali Karate, sannan Sheikh Muhammad Sani Zuru ya gabatar da jawabi na Mauludin, sannan aka bada kyaututuka na wasanin da aka gudanar a taron. 

24th January, 2024