Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

24 Janairu 2024

19:40:06
1432153

Murna Da Haihuwar Imam Ali As 13 ga Watan Rajab A Dakin Ka’abah

Fatima bint Asad mahaifiyar Amirul (As): Ya Ubangiji! Ni na yi imani da kai da abunda ya zo daga gareka na daga manzani da littafai’ kuma ina mai gaskatawa da zancen kakana Ibrahimul-Khalil As, kuma lalle shi ya gina dadadden gida, don hakkin wanda ya gina wannan gida, da hakkin jarirai a cikina, ka saukaka min haihuwata.


 

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku bayanai dangane da haihuwa da kuma rayuwar Imam Ali As wanda a Ranar Juma’ah 13 g watan Rajab shekara ta 10H.

 

Imam Ali dan Abi Dalib AS mahaifiyarsa itace Fadimat bint Asad bin Hashim An haifeshi ne a cikin dakin Ka'aba a Makkah a ranar Juma’ah  goma sha uku ga watan Rajab, shekaru goma kafin aiko Manzo, shekaru talatin bayan Shekarar Giwa,.

 

Shine farkon wanda ya fara Imani da Annabin Rahama AS kuma ya bashi kariya ako daa yaushe Jarumin jarumai miji ga Sayyidah Fadimah AS uba Ga Shugabannin Samarin Aljannah Imam Hasan da Husain AS Mai raba wuta da Aljannah  Farkon Kalifa Imami da  Annabin rahama yabarwa Al’ummarsa Mafi girman Halinta Bayaga Manzon duniya da lahira wanda aka ruwaito falalarsa da darajarsa adukkan littafan masana na duniya gaba daya.

 

Lakubbansa:

أمير المؤمنين، إمام المتّقين، قائد الغُرّ المُحجّلين، يعسوب الدين، الأنزع البطين، سيّد الأوصياء، أسد الله الغالب، المرتضى، حيدر.

Alkunyarsa:

أبو الحسن، أبو الحسين، أبو السبطين، أبو الريحانتين، أبو تراب

Wanda yanayin haihuwarsa da labarin yadda mahaifaiyarsa tayi lokacin da tazo haifarsa ya isa tabbatar da Imaninta da Allah buwayi da kasancewarsu Masu bautawa Allah shi kadai bisa Addinin Annabi Ibrahim da Annabawan gaba daya.

 

An karbo daga Yazid dan Qan’ab ya ce: “Na kasance tare da Abbas dan Abdul Muddalib da tare da wasu gungun mutane daga Bani Abdul Uzza a gaban dakin Allah mai alfarma, sai Fatima bint Asad mahaifiyar Amirul (As) ta zo, ta kasance tana dauke da cikinsa na tsawon wata tara, alamun nakuda sun kamata, sai ta ce: Ya Ubangiji! Ni na yi imani da kai da abunda ya zo daga gareka na daga manzani da littafai’ kuma ina mai gaskatawa da zancen kakana Ibrahimul-Khalil As, kuma lalle shi ya gina dadadden gida, don hakkin wanda ya gina wannan gida, da hakkin jarirai a cikina, ka saukaka min haihuwata.

 

Sai Yazid ya ce: sai na ga gidan ya tsage ta bayansa, sai Fatima ta shiga cikinsa, sai ta bace daga ganinmu, sai ginin ya koma yaa hade yadda yake a asali, bangayen sun, (wanda har yanzu wanna tsagewar tana nan ajikin dakin Ka’abah) sai mu kaai kokarin bude kofar dakin da makullin kofar, amma sai kofar taki budewa, don haka muka fahimci cewa wannan lamari ne daga Allah Ta’ala, sai ta fito a rana ta hudu tana dauke a hannunta jaririnta Amiraal muminina Ali bin Abi Talib. Sai ma bada bushara labari ya ruga zuwa ga Abu Talib da iyalansa, ya gaya masu suka taho da sauri tare da mutane fuskokinsu cike da farinciki, sai Annabi Muhammadul Musdafa (SAWA) ya ya gabato ya rungume shi a kirjinsa, sai ya kai shi gidan Abu Talib – inda a wannan lokacin ma’aiki ya zauna tare da Khadija a gidan baffansa tun aurensa, sai Abu Talib ya sanya a ransa ya sanya wa dansa suna Ali, haka kuwa ya sanya masa. Sayyid Abu Talib ya gudanar da bukin walima na girmama jarirai mai albarka, kuma ya yanka dabbobi masu yawa.

 

Imam Ali as ya samu tarbiyya daga Manzon rahama ne tun daga yarintarsa har girmansa:

Imam Ali As ya aure Sayyidah Zahra’ As diya daya tilo ga Manzon rahama SAWA wand Allah ta’ala ya daura auren su a sama sannan aka daura a doron kasa:

 

Yayansa:

 

الإمام الحسن، الإمام الحسين، زينب الكبرى، زينب الصغرى (أُمّ كلثوم)، المحسن السقط، العباس، جعفر، عبد الله، عثمان، عمرالأطرف، محمّد الحنفية.

Ya rayu shekara 63, imamancinsa ya dauki shekara 30, gwamnatin sa ta dauki tsawon shekara 4 ne.

Imama Ali As ya halarci dukkan yakokin Manzon Allah (S A W), banda yakin Tabuka, a lokacin Manzon (A.S) ya bashi umarnin zama a Madina domin kulawa da ita.

Dangane da yake-yake da shi da kansa ya jagoranta a lokacin halifancinsa (S), sun hada da: yakin Jamal, Saffain, Nahrawan

 

Ya yi shahada a ranar ashirin da daya ga watan Ramadan shekaru 40 bayan Hijira a garin Kufa, kuma an binne shi a wurin da ake kira Al-Ghari da ke Najaf.