Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

24 Janairu 2024

11:24:30
1432065

Za A Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Mai Taken: "Imam Ali (AS) A Nazarin Malaman Da Ba Musulmi Ba" A Kasar Italiya

Bisa daukar nauyin kungiyar hadin kan shi'a ta kasa a Italiya za ta gudanar da taro dangane da Imam Ali (AS) karo na 9 da taken "Imam Ali (AS) a nazarin malaman da ba musulmi ba".

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa:  za’a gudanar da taron Imam Ali (a.s.) karo na 9 mai taken "Imam Ali (a.s.) a nazarin malaman da ba musulmi ba" wanda zai gudana ne karkashin daukar nauyin kungiyar cibiyoyin Shi'a na kasar  Italiya.

Wanda zai karbi bakuncin taron shine Dr. Sayyid Ali Husaini, mataimakin kodinetan kungiyoyin addinin Islama a kasar Switzerland, da Farfesa Christopher Klohesi, Farfesa na Cibiyar Nazarin Larabci da Musulunci da ke birnin Rome na kasar Italiya, Farfesa Paolo Branca, masanin addinin Islama kuma Farfesa na darikar Katolika a Jami'ar Milan, Italiya, da Farfesa Giancarlo Anello, farfesa a Jami'ar Parma, za su gabatar da ra'ayoyinsa.

Za a gudanar da taron "Imam Ali (A.S.) A Nazarin Malaman Da Ba Musulmi Ba" a ranar Asabar 27 ga watan Janairun 2024 (7 ga Bahman 1402) da karfe 17:00 agogon Turai, kuma masu sha'awar halartar wannan taro zasu iya ziyartar Adireshin:

 (https://us04web.zoom.us/j/71485364285?pwd=bXScvpYOLXPVajYh1ebCSe9Im882Q4.1