Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

22 Janairu 2024

13:43:13
1431517

An Bude Ƙungiyar Fatimatuz Zahra A Babban Birnin Madagascar + Hotuna

A yayin wani biki tare da halartar wasu jiga-jigan 'yan Shi'a na Afirka, an kaddamar da kungiyar Fatima Zahra a babban birnin Madagascar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a yayin wannan biki da ya samu halartar wasu mabiya Shi'a na Afirka, an bude kungiyar Fatima Zahra (AS) a Antananarivo, babban birnin kasar Madagascar.

Wannan kungiya na da nufin tsara ayyukan mata musulmi mabiya mazhabar shi'a a kasar Madagaska da bunkasa tare da tallafawa mata da kananan yara a fannonin zamantakewa, ilimi, tattalin arziki, al'adu da addini wannan yunkuri ya samu ne da ɗaukar nauyin 'yan uwa mata mabiya Ahlul Baiti (AS) da goyon bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) an kafa Bayt (AS) Ta Duniya.

Gudanar da kwasa-kwasan koyar da sana'o'i daban-daban kamar dinki, biredi, girki da sana'oin hannu da koyar da harsunan waje da gudanar da taruka, na tattalin arziki da na addini, taimakon tsofaffi da yara marayu, taimakawa matasa wadanda suka kammala karatu samun aikin yi, samar da ayyukan yi ga matasa, na daga cikin shirye-shiryen wannan shirin.

Idan dai ba a manta ba, Ayatullah Riza Ramizani babban shugaban majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya jaddada kasancewa da halartar matan Shi'a a cikin zamantakewar al'umma da kuma kafa majalisar mata a ziyarar da ya kai yankin gabashin Afirka a baya-bayan nan.