Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

22 Janairu 2024

13:26:02
1431510

Ci Gaba Da Bukukuwan Murnar Haihuwar Imam Muhammadul Jawad As

TAQAITACCEN TARIHIN IMAM JAWAD (A.S)

Hadisai 250 ne kawai a ka iya samo wa daga Imam Jawad (A.S), wanda hakan ya samo asali ne ganin cewa shekarun da ya rayu ba su da yawa, haka kuma yana karkashin matsin lambar mahukunta ne. Haka ma masu ruwaito hadisai da SahabbanSa ba su wuce mutane 115 zuwa 193 ba. Ahmad dan Abi-Nasr Bizandi, Safwan dan Yahya da Abdul-Azim Hasani suna cikin jimillar Sahabban Imami din.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya ci gaba da kawo maku bayanai daga manyan malaman addini dangane da haihuwa da kuma rayuwar Imam Muhammadul Jawad As wanda a wannan karon ma muna tare da Dr. Sadiq Aliyu wanda yayi takaitaccen bayani dangane wannan munasaba mai dinbin albarka inda ya fara da cewa:

 Muhammad dan Ali dan Musa, wanda ya shahara da sunaye Imam Jawad da Imam Muhammad Taqi, wanda ya rayu tsakanin shekara ta 194 bayan hijira zuwa shekara ta 220 bayan hijira, shi ne Imami na 9 a cikin jerin Imamai 12 da Yan Shi’ah suka yi imani da su. al-kunyarsa Abu Ja’afar ne, sannan ana masa laqabi da Jawad da ‘Dan Ridha. Dalilin da ya sanya a ke masa lakabi da Jawad kuwa don ya kasance mai yawan kyauta ne da karamci.

Imam Jawad Ya dauki tsawon shekaru 17 Yana yin Imamanci, wanda Ya yi zamani da Khalifofi Ma’amun Abbasi da Mu’utasim Abbasi. Bisa bayanan madogarori da dama, Imam Jawad (A.S) a karshen watan Zul-Qa’ada, shekara ta 220 bayan hijira, Yana mai dan shekaru 25 a duniya, Ya yi shahada. A cikin jerin Imaman Shi’ah, Shi ne wanda Ya yi shahada da mafi karancin shekaru. An binne Shi a kusa da kabarin kakansa Musa dan Ja’afar (A.S) a makabartar Quraishawa da ke Kazimain.

Kasancewar Yana da karancin shekaru (8) a lokacin da Ya zama Imami, ya zama dalilin da ya sanya wasu daga Sahabban Imam Ridha (A.S), suka samu shakka a Imamancinsa: wasu sun bi Abdullahi dan Musa dan Ja’afar, wanda Ya shahara da suna Abdullahi Aukalani, a inda wasu kuma suka bi Ahmad dan Musa Shahcherag, a inda suka dauke su Imamansu. Wasu tawagar kuma sun hade da tawagar da a ke ce musu Waqifiyyah; wanda wasu ne daga cikin Yan Shi’ah suka dauki cewa Imamanci Ya kare ne a kan Imam Musal-Kazim (A.S), amma mafi yawan Sahabban sun karbi Imamancin Muhammad dan Ali (A.S).

Ya kasance alakar Imam Jawad (A.S) da Yan Shi’ah yawanci ta hannun wakilanSa ne, kuma ana yin hakan ne ta hanyar rubuta wasika. A zamanin ImamancinSa, kungiyoyin Ahlul-Hadis (wadanda suka ba wa hadisi girma na musamman), Zaidiyyah, Waqifiyyah da Gullat sun yawaita da ayyukansu. Imam Jawad (A.S) Ya umarnci Yan Shi’anSa da kada su bi irin wadannan sallah, sannan su dinga tsinewa gullatun da suke ba wa Imam Ali (A.S) matsayin ALLAH (S.W.T) ko na Annabta.

Daga cikin shahararrun tattaunawar ilimi wanda Imam Jawad (A.S) Ya yi da malaman bangarori daban-daban na Musulunci akwai mas’aloli na Aqida, haka ma da mas’aloli na Fiqihu irin su hukuncin yanke hannun ‘barawo da hukunce-hukuncen aikin hajji.

Hadisai 250 ne kawai a ka iya samo wa daga Imam Jawad (A.S), wanda hakan ya samo asali ne ganin cewa shekarun da ya rayu ba su da yawa, haka kuma yana karkashin matsin lambar mahukunta ne. Haka ma masu ruwaito hadisai da SahabbanSa ba su wuce mutane 115 zuwa 193 ba. Ahmad dan Abi-Nasr Bizandi, Safwan dan Yahya da Abdul-Azim Hasani suna cikin jimillar Sahabban Imami din.

A cikin madogarorin Shi’ah, an ruwaito karamomin da suka hada da yin magana a lokacin da a ka haife shi, tafiya zuwa waje mai nisa a cikin kankanin lokaci, warkar da marasa lafiya da kuma idan ya yi addu’ah take a ke amsa. Malaman Ahlussunnah ma sun yi bayani kan Shi, ilimin Shi, nitsewa a irfani, sannan suna girmama Imam Jawad (A.S).

Fiye da littattafai 600 na ilimi ne a ka rubuta dangane da Imami na tara a cikin yaruka daban-daban, a ka kuma yada.

Dr. Sadiq Aliyu Musa

22/01/2024