Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

22 Janairu 2024

09:21:33
1431435

Murnar Zagayowar Haihuwar Imam Muhammadul Jawad Dan Aliyur Ridha As

Muhammad bin Ali bin Musa bin Jaafar, wanda aka fi sani da Jawadul A'immah (195-220 AH), shi ne limami na tara daga cikin Imaman shiriya goma sha biyu, kuma ya dau shekaru 17 yana imamancin Al’ummah .

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya maku takaitaccen tarihin haihuwar Imam Jawadul A'imma As:

Muhammad bin Ali bin Musa bin Jaafar, wanda aka fi sani da Jawadul A'immah (195-220 AH), shi ne limami na tara daga cikin Imaman shiriya goma sha biyu, kuma ya dau shekaru 17 yana imamancin Al’ummah . 

An haifeshi ne a Madina 10 ga watan rajaba shekara ta 195 bayan Hijira, kuma yana da shekara takwas lokacin da yakama ragamar imamanci bayan shahadar mahaifinsa Imam ALiyu Al-Rida (As) Kuruciyarsa ta sa wasu gungun sahabban Imam Al-Ridha (A.S) suka yi jinkirin bai'ah ga imamancinsa, amma galibin ‘yan Shi’a sun yi imani da shugabanci da imamancinsa bayan Mahaifinsa (SAW).

 Imam Al-Jawad (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a shekara ta 215 bayan hijira. Ko (214 AH) ya auri ‘yar al-Ma’mun al-Abbasi, Ummu-Fadl. An yi auren ne bisa bukatar al-Ma'mun, don haka Imam al-Jawad (a.s) ya yarda da hakan kuma ya sanya mata sadaki ririn na Sayyadah Zahra (a.s), ma'ana dirhami 500. Umm Al-Fadl ba ta haihu da Imam (A.S) ba, dukkan‘ ya’yan imam din sun kasance daga matar sa, Samanatul magrabiyyah.

Sheikh Al-Mufid ya ambata a cikin Al-Irshad cewa Imam Al-Jawad (A.S) yabar yaya da suka hada da Ali, Musa, Fatimah, da Umama. Wasu malaman sun ambata cewa ‘ya’ya mata na imam mata uku ne: Hakima, da Khadija, da Ummu Kulthum

 A lokacin rayuwar Imam Al-Jawad (amincin Allah ya tabbata a gare shi), an yi muhawara da yawa tsakaninsa da malaman fadar daular Abbasawa dama ma’abuta addinai, hatta suma kansu yan shiah da sukayi kokwanto bisa imamancinsa bayan sunmasa wasu tambayoyi sun dawo sunshi bayan yabasu amsoshi gamsassu akan tambayoyin da sukayi masa kuma anbatason yazo acikin hadisai da yawa a cikin littattafan hadisi (SAW) da suka hada da mas’alolin koyarwa, fassarar Alkur'ani da bangarori daban-daban na fikihu. Kuma ya kasance yana sadarwa tare da ‘yan Shi’arsa ta hanyar wakilansa ta hanyar wasiku.

Ashekarata 220AH akarshen watan rajab Yana da shekaru 25 yayi shahada a birnin Bagadaza, wanda ya shahadantar shi ne khalifah Al-Mu'tasim Al-Abbasi. Kuma shine mafi karancin shekaru cikin imaman Ahlul-baiti AS lokacin da ya yi shahada, an binne shi a Kadhimiya kusa da kabarin kakansa Imam Musa bin Jaafar (a.s)