Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

20 Janairu 2024

12:05:28
1430826

Kwamandojin IRGC 4 Sun Yi Shahada A Harin Da Isara'ila Ta Kai Damascus + Bidiyo

Kafofin yada labarai sun tabbatar da shahadar mashawartan Iraniyawa hudu a harin da gwamnatin sahyoniya ta kai a Damascus a safiyar yau Asabar.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Wasu kwamandoji da mashawarta na Iran sun yi shahada a harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a wani yanki da ke birnin Damascus na kasar Siriya.

Kamar yadda sanarwar IRGC ta biyo bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai Damascus

Ma'aikatar Hulda da jama'a ta dukkan sojojin Iran:

A halin da ake ciki kuma gwamnatin Sahayoniyya mai aikata muggan laifuka ta kai hari birnin Damascus fadar mulkin kasar Sham, kuma a yayin farmakin ta sama da mayakan mamaya na gwamnatin 'yan ta'addan suka kai, an samu shahadar da dama daga cikin sojojin Siriya da mashawartan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran 4.

Za a sanar da ƙarin bayani daga baya...