Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

17 Janairu 2024

12:52:34
1430147

Shaikh Zakzaky Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Da Yahudawan Sahyoniya Ke Wa Duniya

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky Hf ya yi gargadin cewa masu kashe Falasdinawa na iya kara kai hare-hare ga duniya baki daya, domin neman cikakken iko.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi gargadin cewa masu kashe Falasdinawa na iya kara kai hare-haren mamaya ga duniya baki daya, domin neman cikakken iko.

Sheikh Zakzaky, yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Press TV ya ce dangane da mayakan da ke gwagwarmaya a Gaza: “Masu yaki a Falasdinu suna gwagwarmaya ne ba don ‘yantar da Falasdinu kadai ba, a’a, suna fafutukar gwagwarmaya ne don ‘yantar da dukkanin wadanda ake zalunta a duniya baki daya”.

Dangane da yakin da Isra'ila ke ci gaba da yi, Shaikh Zakzaky ya yi Allah-wadai da irin zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, inda ya ce, "Halayyarsu ta wuce ta namun daji".

Ya jaddada cewa kungiyoyin gwagwarmaya da ke yaki da gwamnatin Isra'ila ba wai suna fafutukar 'yantar da Falasdinu ne kawai ba, har ma suna fafutukar kwato 'yancin mutanen da ake zalunta a duniya.

Ya ba da shawarar cewa masu acikin yakin suna wakiltar muradun kowane musulmi ne dama dukan mutane. Bugu da kari, ya yi gargadin cewa idan yahudawan sahyoniya suka yi nasara a ayyukan da suke yi a kan musulmi, to mai yiyuwa ne za su kara fadada kai hare-hare kan sauran gungun al'umma a duniya.

Shaikh Zakzaky ya yi karin haske kan irin yadda aka samu asarar mutane wacce ta wuce misali, inda kashi 70% mata ne da kananan yara.

Shaikh Zakzaky ya mika godiyarsa ga al’ummar duniya kan goyon bayan Palastinu, inda ya yi nuni da gagarumin zanga-zangar da ake gudanarwa hatta a Amurka da Turai.

Sheikh Ibrahim Zakzaky, an haife shi a shekara ta 1953, sanannen malamin addinin Musulunci ne kuma jagoran Harkar Musulunci a Najeriya. Ya rayu tare da samun tarbiyya da reno daga iyaye malaman addinin Musulunci, ya haddace Al-Qur'ani yana da shekaru 14. Ya yi fice a fannin ilimin Larabci da na Musulunci, daga baya ya karanci tattalin arziki da aikin gwamnati. A cikin gwagwarmayar duniya a shekarun 1970, ya ba da kariya ga Musulunci a matsayin cikakkiyar hanyar rayuwa. Zakzaky ya kafa Harkar Musulunci a Najeriya a shekarun 1980, inda ya fara tun yana matashi amma a yanzu yana da miliyoyin mabiya daban-daban da suka hada da kiristoci da daidaikun mutane masu bambancin addini.