Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

15 Janairu 2024

15:34:41
1429665

An kaddamar Da Babar Mai Dauke Da Rubutu Na Musamman Ga Shahidai 'Yan Jaridar AGaza + Hoto

An kaddamar da wata fastar takarda ta musamman na tunawa da shahidai ‘yan jarida 115 na Gaza a wajen taron tunawa da shahidan 'yan jarida na Gaza da aka gudanar a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da taron tunawa da shahidai na Gaza a yau Litinin 15 ga watan Disamba 2024 a birnin Tehran a karkashin jagorancin kamfanin dillancin labarai na ABNA.

An gudanar da jawaban wannan taron kaitsaye da kuma yanar gizo daga Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) ta Duniya da ministan yada labaran kasar Yemen Daifullah Al Shami da wasu manyan mutane daga cikin kasashen Palastinu, Yemen, Iraki, Turkiyya. , da Indonesiya, tare da kasancewar masu kula da kafofin watsa labarai na duniya da masu fafutuka.

A karshen wannan taro an kaddamar da wata fosta na musamman na tunawa da shahidan 'yan jarida fiye da 115 na Gaza.