Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Janairu 2024

18:29:40
1429365

Sayyid Hassan Nasrullah: Wanda Ya Kamata Ya Ji Tsoron Yaƙi Ita Ce Isra'ila Da 'Yan Share Guri Zauna, Ba Mutanen Lebanon Ba.

Sayyid Hassan Nasrallah: Wai Makiyan Da Suka Sha Kashi Suke Yi Mana Barazana; To Bismillah! Muna Maraba

Babban shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana a cikin jawabinsa na yau cewa: Muna fuskantar barazanar kai mana hari daga bataliyoyin da suka sha kaye a yakin da suke da gwagwarmayar Gaza, muna sanar da su cewa: Bismillahi! Muna maraba Sojojin yahudawan sahyoniya, a lokacin da suke cikin yanayi mai kyau kuma suna cin gajiyar mafi girman makamansu, sun sha kaye a yakin da suke da mu a yakin 2006.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: "Sayyid Hassan Nasrallah" babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a yammacin yau (Asabar) dangane da cika kwanaki bakwai da shahadar Wassam Hassan Tawil wanda ake yi wa lakabi da "Al-Haj Jawad" daya daga cikin kwamandojin wannan yunkuri da yayi shahada a harin da yahudawan sahyuniya ya yi jawabi a kudancin kasar Lebanon.

A farkon jawabin nasa Sayyid Hasan Nasrallah ya yi nuni da cewa, iyalan da suka sadaukar da shahidai a tafarkin tsayin daka gwagwarmaya suna ci gaba da aikewa da 'ya'yansu a fagen daga inda ya ce: dimbin matasanmu suna fada a fagen daga tun kwanaki 100 da suka gabata.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya kara da cewa: Wani bangare na ayyukan jagororin gwagwarmayar da suka yi shahada na daga cikin sirrin gwagwarmayar, kuma wajibi ne mu ba da hadin kai wajen samar da tushen gwagwarmaya da kuma dakewa a wannan yakin, wanda har yanzu ba a san karshensa ba. "

Sayyid Hassan Nasrallah ya ce dangane da shahidi Haj Jawad: Wannan kwamandan gwagwarmaya na daga cikin kwamandojin fagen yaki a shekara ta 2006. Ya kuma kasance a Siriya a matsayin daya daga cikin kwamandojin yaki da ISIS.

Da yake bayyana cewa kungiyar Hizbullah tana alfahari da yaki da kungiyar ISIS da kuma bayar da shahidai a wannan fagen, ya kara da cewa: Haj Jawad ya kasance daya daga cikin manyan kwamandojin fagen gwagwarmaya a kudancin kasar Lebanon tun daga ranar 8 ga watan Oktoba (16 Mehr) zuwa da abun ya biyo baya. Yana mai kaunar shahada kuma ya cimma burinsa.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin jarumtaka da gwagwarmayar da al'ummar Gaza suka yi a cikin kwanaki 100 da suka gabata, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Al'ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar matakin wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan ta hanyar salon da ba a taba ganin irinsa ba, kuma acikin yanayin yin shiru da boyewar da kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya, kafofin yada labaransu sun taka muhimmiyar rawa wajen sanar da kokarinsu.

Sayyid Hasan Nasrallah ya yi ishara da cewa: Bayan yakin kwanaki 100 a Gaza da kuma yakin guguwar Aqsa, gwamnatin sahyoniyawan tana cikin nutsewa da gazawa, kuma a cewar manazarta, ta fada cikin wani rami mai zurfi, kuma ba ta cimma burinta na wata nasara ko ma samun kishi-kishin nasarar ba.

Babban shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ya yi nuni da cewa gwamnatin Yahudawan ba ta cimma wani burin da ta ayyana ba kuma hakarta ba ta cimma ruwa ba, yana mai jaddada cewa, makiya za su ci gaba da fafutukar ganin sun cimma dukkanin nasarori kafin shiga mataki na uku na yakin da kuma janyewar sojojinsu.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Asarar da 'yan mamaya suka yi ya kara musu nakasa kwazonsu da gazawarsu, lamarin baya-bayan nan shi ne ayyana nakasassu na sojojin mamaya da addinsu ya kai 4000 a cikin kwanaki 100 na gwagwarmaya da kansu, kuma adadin na iya karuwa zuwa 30,000.

Babban shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi ishara da cewa: Idan yakin ya tsaya, makiya za su san irin bala'in da ya afku sakamakon gwagwarmaya a Gaza da magoya bayanta a sauran fagagen gwagwarmaya.

Sayyid Hasan Nasrallah ya kuma kara da cewa: Yawan mace-macen 'yan mamaya a fagagen gwagwarmaya a Gaza da yammacin kogin Jordan da kuma kasar Labanon tare da asarar tattalin arziki da kuma nauyin kauracewa gidajen yahudawan sahyoniyawan a cikin yankunan da ake mamaya na karuwa kowace rana.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hare-haren da kasar Yamen ke kai wa jiragen ruwan yahudawan sahyoniya domin nuna goyon baya ga zirin Gaza, ya ce: Abin da ke faruwa a cikin tekun Bahar Maliya cutarwa ce babba ga makiya yahudawan sahyoniya, wadanda fuskarsu ta hakika ta bayyana ga duniya gaba daya a kotun Hague.

Sayyid Hasan Nasrallah ya kara da cewa gabatar da gwamnatin sahyoniyawan mamaya a gaban kotun Hague da kuma zarginta a gaban ra'ayoyin al'ummar duniya, abu ne da ba a taba ganin irinsa ba saboda wasu kwararan dalilai da ya haifar da tashin hankali ga wannan gwamnati.

Har ila yau babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Ta hanyar musanta laifin kisan kare dangi da ta yi wa Palastinawa a Gaza, gwamnatin 'yan mamaya ta yahudawan sahyoniya ta dauki manufar " halin munafunci " a gaban ra'ayoyin al'ummar duniya.

Sayyid Hasan Nasrallah ya yi ishara da cewa iyalan fursunonin yahudawan sahyoniya sun yi watsi da fatansu na ganin an sako su daga wajen yan gwagwarmaya , yana mai cewa: "Isra'ila" sun tabbata cewa majalisar ministocinsu ba ta da wani aiki kwata-kwata don haka ya kamata a cire ta tare da ajiye aikin ministanta.Wannan yana nufin tabbatarwarsu da gazawar.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya kara da cewa: Idan har aka ci gaba da gudanar da ayyukan da ake yi a yankunan gwagwarmaya a Gaza, Yammacin Kogin Jordan, Lebanon, Yemen da Iraki, makiya yahudawan sahyoniya za su amince da sharuddan gwagwarmaya.

Har ila yau babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Amurkawa da wasu kasashen yammacin turai sun yi kokarin dakile wasu fagage a tsawon kwanaki 100 na wuce gona da irin da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a zirin Gaza, yayin da hakan ke nuni da irin tasirin da wasu bangarori suke da shi wajen tinkarar gwamnatin sahyoniyawan wuce gona da ia Gaza. Barazana, tsoratarwa da karfafa gwiwa da ke faruwa a kan Iraki, Yemen, Lebanon, Siriya da Iran.

Yayin da yake ishara da cewa hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen na baya-bayan nan ya nuna wauta irin na Amurka da Ingila da kuma irin cin karo a lamarin Amurka, inda ya yi karin haske da cewa: Amurkawa a wasu kasashe ciki har da kasar Labanon, suna barazana ga 'yan siyasa da ra'ayin jama'a kan wuce gona da iri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Amurkawa yayin da suke kira da kada a fadada yakin suna kara fadada shi, kuma idan har suka yi imani cewa kasar Yemen za ta ja da baya daga matsayinta bayan hare-haren Amurka da Birtaniya, to sun yi kuskure matuka.

Sayyid Nasrallah ya yi nuni da cewa hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen zai haifar da ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa na gwamnatin sahyoniyawa ko kuma wadanda ke nufin yankunan da aka mamaye da kuma lalata zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin tekun Bahar Maliya kuma zai mayar da wannan yanki fagen fama, wanda a zahiri aiki wauta ne .

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya jinjinawa matsayin malamai da al'ummar Yamen wajen goyon bayan al'ummar Gaza da kuma gwagwarmaya da kuma sabawa da matsayi da manufofin gwamnatin wannan kasa Ya ce: Al'ummar Yemen za su yanke shawara kan mayar da martani ga hare-haren da Amurka ke kai wa, kuma Biden da gwamnatinsa za su yanke shawara kan aikewa da sako ga Iran da kuma barazanarsu kan kasar Yemen.

Jagoran gwagwarmayar kasar Labanon ya kara da cewa: Filin yaki da kuma kwanaki masu zuwa za su tabbatar da makomar arangamar da ake yi tsakanin al'ummar kasar Yemen da masu wuce gona da iri, kuma nan ba da jimawa ba Amurkawa za su gane kuskurensu.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce: Ma'aunin gaskiya a wannan fanni shi ne goyon bayan kasar Yemen. Domin kasar Yemen tana goyon bayan Falasdinu da Kudus kuma wadanda ba sa goyon bayan Yemen za su yi kasa a gwiwa ba.

Sayyid Hasan Nasrallah ya ci gaba da cewa: Harin da dakarun juyin juya halin Musulunci na kasar Iraki suka kai a wani wuri a birnin Haifa ta hanyar amfani da makami mai linzamin ruwa wani mataki ne mai inganci kuma gwamnatin yahudawan sahyoniya ta ki bayar da cikakken bayani kan wannan hari na makami mai linzami da aka kaiwa Haifa da kuma irin wannan matakin na boye gaskiya za'a iya fahimtarsa a rashin tabbatarwa da suka yi na cewa makamai masu linzami na gwagwarmaya na Lebanon ne suka kai hari kan sansanin sojojin Miron.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: A baya-bayan nan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Lebanon ta harba makaman roka 62 da suka hada da Katyusha 40 da Kornets 22 a sansanin soji na 'yan mamaya na Miron, inda suka boye irin hasarar da suka yi.

Sayyid Hassan Nasrallah ya kara da cewa: Bidiyon da 'yan adawa suka fitar game da harin da aka kai kan sansanonin Miron da Safad ya fallasa karya da boyewar da mamaya ta ke yi.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin yahudawan sahyoniya tana boye adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata, hasarar kudi da gazawarta domin a cewar kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya, hakan zai haifar da yanke kauna a tsakanin yahudawan sahyoniyawan.

Jagoran gwagwarmayar kasar Labanon ya yi nuni da cewa kungiyar Hizbullah tana ci gaba da tinkarar gwamnatin sahyoniyawan da kuma haifar da hasarar rayuka da barna ga wannan gwamnati, kuma hakan yana haifar da matsin lamba na yahudawan sahyoniyawan suka tserewa daga yankunan da aka mamaye kan majalisar ministocin mamaya.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, Amurkawa sun yi wa kasar Labanon barazana, matukar ba a daina yakin kudancin kasar akan 'yan mamaya ba, to Isra'ila za ta fara yaki da Lebanon. Amma muna gaya musu: Barazanar ku ba za ta yi amfani ba, a yau, ko a gobe, kai har abada.

Sayyid Hasan Nasrallah ya ci gaba da cewa: Muna fuskantar barazanar kai hari daga bataliyoyin da suka gaza a yakin da suke da gwagwarmayar Gaza. Muna yi musu albishir da cewa: Bismillah! Muna maraba Sojojin yahudawan sahyoniya, a lokacin da suke cikin yanayi mai kyau kuma suna cin gajiyar mafi girman makamansu, sun sha kaye a yakin da sukai da mu a yakin 2006.

Babban shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Zai fi kyau Amurkawa da suke nuna cewa suna cikin damuwa game da wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan ke yi wa kasar Labanon su damu da jami'ansu da sansanonin su a yankin domin tun kwanaki 99 da suka gabata a shirye muke da mu yi yaki kuma ba ma tsoronsa."

Sayyid Hasan Nasrallah ya ci gaba da cewa: An fara shiga fagen daga a kasar Labanon ne da nufin goyon bayan zirin Gaza da kuma dakatar da kai hare-haren da take kai wa a Gaza, sannan kuma a lokacin da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza ya tsaya, to za a yanke kudiri akan kowane lamari da ya faru.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya jaddada cewa, tsaron tekun Bahar Rum da kuma kwantar da hankulan bangarorin Lebanon da kuma halin da ake ciki a Iraki ya dogara ne kan dakatar da kai hare-hare a kan Gaza.