Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Janairu 2024

11:18:08
1429283

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM BAQIR (A.S)

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti - Abna bisa zagayowar haihuwai Imam Muhammad Bakirul Ulum As ya kawo maku takaitaccen bayani dangane da wannan munasaba inda ya kawo maku bayani daga babban masanin nan kuma marubuci Dr. Sadiq Aliyu Musa Yola:

Bismillahir Rahmanir Rahiim

Imam Muhammad Baqir (A.S), 'Da ne ga Imam Sajjad (A.S) da Fatima yar Imam Hassan (A.S) dan uwa ga Imam Hussain (A.S). Da yake nasabarsa ta hada ta Imam Hassan (A.S) da Imam Hussain (A.S), ya sa ake masa lakabi da Bahashime a tsakanin Hashimawa biyu, Ba'alawiyye a tsakanin Alawiyyawa biyu da kuma Ba'Fadime a tsakanin Fadimawa biyu.

Bisa ga ruwayar da aka karbo daga sahabi Jabir Dan Abdullahi Ansari, Annabi (S.a.w.a) tun kafin haihuwar Imam Baqir (A.S) ya sanya masa suna Muhammad, sannan ya masa lakabi da suna BAQIR. Daga cikin lakabobinsa akwai "Bakirul-ulum", "Shakir" wato mai godiya, "Hadi" wato mai shiryarwa da "Amin" wato amintacce; amma lakabin sa da yafi shahara shi ne Baqir din, wato mai tsatstsage ilimi da fede shi.

Marubucin littafin Tarihi, Ya'kubi ya rubuta a cikin littafinsa cewa: "dalilin da ya sa ake kiransa da Baqir shi ne yadda yake tsatstsage ilimi da fede shi." Yana da alkunyar Abu Ja'afar wato Baban Ja'afar da ya shahara da ita. Sai dai a littafan hadisi da ruwaya ana kiran sa da Baban Ja'afar na daya don a bambance shi da Baban Ja'afar na biyu wato Imam Jawad (A.S).

An dai haife shi ne a daya ga watan Rajab shekara ta 57 bayan hijira a garin Madina. Amma wasu na ganin an haife shi ne a 3 ga watan Safar na wannan shekarar din ne. Bisa doron tarihi ya auri mata uku ne sannan yana da yara Bakwai daga cikin su ne akwai Imam Sadiq (A.S).

Imam Baqir (A.S) a shekara ta 95 bayan hijira zamanin Imamancinsa ya soma bayan shahadar mahaifinsa. Sannan yayi zamanin imamancinsa ne har zuwa shekara ta 114 bayan hijira, wato shekarar da yayi shahada.

Yayi zamani da Khalifofin Umayyawa biyar, sune: Walid dan Abdulmalik, Sulaiman dan Abdulmalik, Umar dan Abdul Aziz, Yazid dan Abdulmalik da Hisham dan Abdulmalik.

A zamanin Imam Baqir (A.S) jami'ar ilimi ta gidan Annabta ta kankama, wanda kuma ta habaka da bunkasa ne a zamanin imamancin danSA Imam Ja'afar (A.S). Ya ba da ilimi a bangarori daban daban kama daga ilimin kur'ani, na zamani, tarbiyya da dai sauransu. A zamaninsa ne Yan shi'arSa wato mabiyansa suka fara rubuce rubuce a fagage da dama da suka hada da Fikihu, Tafsiri da Tarbiyya.

Almajiransa sun sha ilimi da dama daga gare shi, daga cikin su akwai Jabir dan Yazid Ja'afi, wanda ya ruwaito hadisai dubu 70 daga Imam Baqir (A.S).

Da yake a zamanin Imam Baqir (A.S), gidan Annabta sun samu raguwar takura da zalunci daga mahukuntan wannan zamani yasa ya dinga fitar da ilmummuka na Aqida da kokarin warware karkata da bata da al'umma ke kai. Daga cikin abubuwan da ya tattauna akwai gazawar hankali wajen gano HAKIKANIN Allah Madaukakin Sarki, kasancewar Allah wanzajje wanda ba zai taba gushewa ba da kuma wajibcin yiwa Imam (A.S) biyayya.

Yayi tattaunawar ilimi da dama da mutane daban-daban wadanda a waccan zamanin ana ganin sune kurewa da tikewa a fagen ilimi.

Hakanan yayi gwagwarmayar tsame tatsuniyoyin yahudawa a cikin abubuwan da ya shafi addinin musulunci, wanda a waccan zamanin sun shiga cikin musulmai suna dasa tatsuniyoyinsu domin cutar da addinin Allah.

Imam Muhammad Baqir (A.S) shi ne Imami na biyar a cikin jerin imamai 12 da Manzon Allah yayi busharar wanzuwarsu a doron kasa.

Muna amfani da wannan dama wajen yiwa daukacin muminai da ma masoyan Ahlul-Bayt (A.S) taya murnar zagayowar ranar haihuwar wannan Imami mai daraja. ALLAH ya sa mu a cetonsa, albarkacin Manzon Allah s.a.w.a da iyalan gidansa tsarkaka.

Dr. Sadiq Aliyu Musa

13/01/2024