Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Janairu 2024

10:38:21
1429270

An Kashe Sojojin Yahudawan Sahyoniya 522 A Yakin Gaza

Adadin sojojin Isra'ila da aka kashe a yakin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 522 kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 2486.

A cewar kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) - Abna - Sojojin Isra'ila sun sanar a safiyar yau Lahadi cewa an kashe daya daga cikin sojojinsu tare da raunata wani jami'i a wani gumurzu da aka yi a kudancin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij Online cewa, rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar da cewa an kashe wani soja mai shekaru 21 da haihuwa, yayin da wani jami'i guda ya samu munanan raunuka sakamakon gumurzun da aka yi a kudancin zirin Gaza.

A jiya ne dai rundunar sojin Isra'ila ta sanar da mutuwar daya daga cikin sojojinta tare da raunata jami'anta biyu da wani soja daya a Gaza.

Ta wannan Karin mutuwar, adadin sojojin Isra'ila da suka mutu ya kai mutane 522, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 2486 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da fafatawa a zirin Gaza; Yakin da ya shiga kwana 100 a yau, wanda yakin ya yi sanadin shahadar mutane 23,843 da kuma jikkata mutane 60,317 na al’ummar Falasdinu.

 

.................