Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Janairu 2024

10:30:29
1429267

Ƙididdigar Mafi Yawan Zubar Da Jini A Cikin Tarihin Sabbin Yaƙe-Yaƙe

Falasdinawa Dubu Dari Ne Da Yakin Kwanaki 100 Da Aka Yi Da Gaza Ya Rutsa Da Su.

A Rana ta 100 na mamayar gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza Palastinawa 100,000 abun ya shafa daga ciki akwai wadanda su kai shahada, ko jikkata ko kuma suka bata sakamakon kisan gillar da aka yi a wannan yanki.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: bias nakaltowa daga kamfanin labarai na -IRNA- Kungiyar kare hakkin bil'adama mai zaman kanta ta Turai - Mediterranean a cikin wani rahoto da ta fitar a rana ta 100 na mamayar gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza ta sanar da cewa Palastinawa 100,000 abun ya shafa daga akwai wadanda su kai shahada, ko jikkata ko kuma suka bata sakamakon kisan gillar da aka yi a wannan yanki.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA na kasar Iran ya habarta cewa, a cikin wannan rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta nahiyar Turai da Mediterranea ta sanar da cewa: Tel Aviv ta hanyar aikata munanan laifuka, ta kashe akalla Palasdinawa dubu daya a kowace rana, wanda shi ne kididdiga mafi muni a cikin tarihin sabbin yakuna.

Wannan kungiyar kare hakkin bil'adama ta kara da cewa: an fitar da rahotan cewa Kashi 92 na wadanda yakin Gaza ya rutsa da su 'yan kasa ne da fararen hula, daga cikinsu akwai kananan yara 12,345 da ba su ji ba ba su gani ba, mata 6,471, ma'aikatan lafiya 295, jami'an tsaron farar hula 41, da kuma 113 yan jarida.

A cewar wannan kungiya, Falasdinawa 1,955,000 ne aka tilastawa barin gidajensu a zirin Gaza ba tare da wani matsuguni ba, wanda ya kai kashi 85% na al'ummar Gaza.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Turai da Mediterranean ta jaddada cewa gwamnatin sahyoniyawan tana kai hare-hare kan ababen more rayuwa na zirin Gaza da nufin mayar da yankin da ba shi da matsuguni kuma ba ta kebe ko da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu da masallatai daga hare-haren ta.

A baya dai wannan kungiyar kare hakkin bil'adama ta sanar da cewa a cikin wani rahoto da ta fitar dangane da laifuffukan yahudawan sahyuniya: Falasdinawa da suka tsira daga hare-haren bama-bamai da kuma hare-haren da ake kaiwa ta kasa da ruwa da ta sama na gwamnatin sahyoniyawan na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon rashin magunguna.

Ofishin yada labarai na hukumar Falasdinu a zirin Gaza kuma ya sanar a yau Lahadin cewa, tun bayan fara yakin mutane 7,000 ne suka bace kuma suka kasance a karkashin baraguzan gine-gine sakamakon hare-haren da makiya yahudawan sahyoniya suka kai a wannan yanki.

A halin da ake ciki kuma, ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da shahadar Palasdinawa dubu 23 da 843 a zirin Gaza a ranar Asabar din da ta gabata inda ta kuma jaddada cewa a cikin wannan lokaci mutane dubu 60 da 317 ne suka jikkata.

Yayin da aka kwashe kwanaki dari da fara kai hare-haren guguwar Al-Aqsa, da kuma fara aikata laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a zirin Gaza, Tel Aviv ba ta cimma burinta ba, sai dai na kisan kare dangi, sannan kuma an asarar dala biliyan 60 na durkushewar tattalin arziki, ga kuma hasarar da tai na sojoji, ga guguwar kashe-kashen kai da kai, da shige da ficen yin hijira da dai sauransu da alhakinsa ya doru akan wannan gwamnati.

 

Kwanaki 100 ke nan da fara aikin guguwar Al-Aqsa da aka gudanar a ranar 7 ga Oktoba (15 Mehr). Wani farmaki da ya fallasa raunin tsarin leken asiri da tsaro na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da ruguza mulkin mallaka na Isra'ila.

Kawai nasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta samu a wannan lokaci ita ce kisan kiyashi da shahadantar da mutane fiye da dubu 23 da kuma jikkata wasu fiye da 60,000. Batun da ya fuskanci martani a duniya kuma fiye da kasashe dari sun shiga cikin zanga-zangar.

A yayin da ake samun karuwar shahidai a Gaza, matsin lambar da ake yi wa Netanyahu da ke buga gangunan ci gaba da yakin neman dawwama a kan mulki ya karu.