Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

11 Janairu 2024

17:44:45
1428591

Yadda Netanyahu Ya Nuna Fushinsa Akan Afirka Ta Kudu Da Kotun Kasa Da Kasa

Iran: Muna Goyon Bayan Bajintar Da Kasar Afrika Ta Kudu Ta Nuna Kan Gwamnatin Sahyoniya

Bidiyon Yadda Netanyahu Ya Nuna Fushinsa Akan Afirka Ta Kudu Da Kotun Kasa Da Kasa

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ministan harkokin wajen Iran Amir Abdullahian ya ce: Muna matukar goyon bayan matakin jajircewa da gwamnatin Afirka ta Kudu ta dauka kan gwamnatin sahyoniyawan da ke kashe kananan yara inda ta takai kararta a gaban kotun duniya.

A sashe guda kuma bayan kammala zaman farko na karar da Afrika ta Kudu ta shigar kan gwamnatin sahyoniyawan kan kisan kiyashin da take yi a zirin Gaza a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, Benjamin Netanyahu a fusace da kakkausar murya ya yi martani ga Afirka ta Kudu da kotun tare da kiran sojojin gwamnatinsa. "mafi kyawawan halin kirki Sojojin duniya!

Firaministan yahudawan sahyoniya ya yi iƙirarin cewa: A yau duniyarmu ta juye kuma muna yaƙi da 'yan ta'adda da makaryata.

Shi ya fusata da karar shari'ar gwamnatin sahyoniyawan ya kara da cewa: muryar munafuncin Afirka ta Kudu ta yi a banza.

Netanyahu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kare abin da ya kira "yancin kare kansa da kuma tabbatar da makomarta har zuwa cikakken nasara."

A mayar da martani ga sauraron karar kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta yi a kotun Hague, ya yi da'awar cewa: Sojojin Isra'ila, wadanda su ne sojojin da suka fi da'a a duniya, ana tuhumarsu da laifukan yaki.