Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

10 Janairu 2024

17:08:43
1428280

Bidiyon Yadda Aka Raka Gawar Shahid Wassam Tawil Babban Kwamandan Kungiyar Hizbullah

Bidiyon Yadda Aka Raka Gawar Shahid Wassam Tawil Babban Kwamandan Kungiyar Hizbullah

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Mayaka da magoya bayan kungiyar Hizbullah sun halarci taron jana'izar Wassam Tawil daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Hizbullah a garinsu na Kharbe Salam da ke kudancin birnin Beirut. Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin cewa, Wassam Hassan Al-Tawil wanda aka fi sani da Haj Jawad daya daga cikin kwamandojin gwagwarmayar kasar Lebanon ya yi shahada a kan tafarkin taimakawa birnin Kudus. Ya yi shahada a harin da jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan suka kai masa.