Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Janairu 2024

18:22:35
1428044

Manufar Makiya Ita Ce Kawar Da Mutane Daga Fagen.

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Hasashen Nasarar Gwagwarmayar Palastinawa Na Gab Da Tabbatuwa

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki yunkurin rage halartar mutane a muhimman munasabobi a matsayin daya daga cikin dabarun makiya na kawar da mutane daga fagen addini yana mai cewa: yin izgili da jerin gwanon Arba'in, sanya shakku kan mutuntawar da mutane suke yi ga babban kwamandan Iran da kuma al'ummar yankin, da kuma haifar da shakku kan halartar mutane masu girma a cikin bukukuwan addini kamar nisfu Sha'aban na daya daga cikin misalan dabarun makiya na fitar da mutane daga cikin fagen addini.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku fassarar cikakken bayani Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar yau din nan ne a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar yunkuri mai dimbin tarihi na al'ummar Qum a ranar 19 ga watan Day shekara ta 1356 a wata ganawa da dubban al'ummar wannan birnin, yana mai nuni da irin karfi na musamman na irin rawar da mutane suke da shi, shiga gaban wajen riko da tuta na al'umma a kowane fagege, da dabaru masu tasiri da bayyanar da tafarkin Imam Khumaini da tsarin Musulunci; ya kira kawar da mutane daga fagen addini, dabarun makiya tsarkakkiyar kasa ta Iran, musamman Amurka da yahudawan sahyoniya, ya kuma jaddada cewa: Kowane mutum a ko'ina yana da harshe mai fa'ida, inganci da ake saurarensa da shi, wanda ya kamata ya kira mutane su shiga cikin fagage daban-daban na siyasa, tattalin arziki, al'adu da sauran su ta hanyar haɓaka ilimi.

Ayatullah Khamenei ya kira birnin Qum birnin a matsayin birnin Yunkuri da ilimi da jihadi, sannan kuma ya yi ishara da darussa masu dawwama na yunkurin muminai na wannan gari a ranar 19 ga watan Day shekara ta 1356 yana mai cewa: Wannan lamari mai girma da ya faru domin nuna adawa da Matakin da gwamnatin kasar ta dauka na buga labarin batanci ga Imam, hakan ya tabbatar da irin karfin da mutane ke da shi na taka rawa a cikin manyan al'amura.

Ya dauki Gaza a matsayin wani kwakkwaran misali na wannan gagarumin karfi na al'umma yana mai cewa: Wasu tsirarun mutane a wata karamar kasa sun yi galaba a kan Amurka da dukkanin ikrarinta da kuma gwamnatin sahyoniyawan da ta dogara da Amurka da karfin hakuri da gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da hambarar da gwamnatin Tagutu azzaluma a cikin shekara guda bisa tasirin yunkurin mutanen Kum a matsayin wani tabbataccen sakamako na halartar mutane a fage yana mai cewa: Imam mai girma ya koyar da wannan babban darasi ga al'umma a cikin shekaru 41 da 42 ta hanyar magana da aiki.Ya nuna halartar mutane a fage abin al'ajabi ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki dogaro da talakawan al'umma a matsayin zabin Imam ta hanyar bin hanyoyin siyasa na gama gari da suka hada da zama da tsayawa da jam'iyyun siyasa da masu fada a ji, sannan ya kara da cewa: Imam ya bayyana a fage ne a ranar 12 ga watan Khordad 42 a makay Faiziyyeh kuma gayyato dinbin jama'a a dandalin tare da basu tuta a hannunsu, inda ya zamo zanga-zangar da al'ummar kasar suka yi a ranar 15 ga watan Khordad 42 a Tehran, Qum, Varamin da sauran garuruwa, shi ne amsar al'ummar kasar kan wannan kira.

Ya dauki wannan yunkuri na mutanen Kum da aka yi a ranar 19 ga watan Day a matsayin amsa ga darasin da Imam ya bayar ga al'umma domin halartarsu a ko yaushe a fage yana mai cewa: Dogaro da mutane ko shakka babu darasi ne na Amirul Muminin, wanda yake cewa a Nahjul Balagha cewa yawan al'umma su ne goyon bayan addini, kuma sune babban ginshikin al'umma kuma tanadin wajen yin gaba da gaba da makiya.

Ayatullah Khamenei ya soki wadanda ke kiran halartar shugaban kasa a tsakanin al'umma da suke ce masa ɗan rayi (Populism) da cewa: mutane sun ne babban ginshiki na asali na manufofin tsarin, ingancin aiki tare da ɗimbin jama'a babbar fasaha ce da yakamata a yi la'akari da ita. Alokacin da mutane ya zamo sun samu halarta za'a samu sauƙin rauni a wasu wuraren.

Ya dauki " san jin tsoro masu girman kai da Amurka da gwamnatin sahyoniyawa" a matsayin wata dabara ce ta fitar da al'umma daga fage yana mai cewa: Idan da a ce al'ummar Iran suna tsoron wani karfi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta wanzu ba, alhali a yau da yawa daga cikin masu da'awar mulki da fifiko a kan yankin, suna tsoron al'ummar Iran.

Ayatullah Khamenei ya kira sauran hanyoyin da baki Makiya suke bi wajen kawar da mutane daga fage da cewa: sanya mutane suji ba za su iya yin imani da abubuwan da suka shafi kasantuwarsu ba, da jajircewa da karfi, yana mai cewa: Imani da shari'a su ne manyan abubuwan da ke haifar da karfi, kokarin makiya da kuma farfaganda ana yin su ne da nufin raunana wadannan abubuwa

Ya kara da cewa: Ya kamata mu mai da hankali kuma mu yi aiki kan lamarin hijabi da ire-irensa tare da ganin cewa matsalar ba wai jahilcin da wasu suke da shi ba ne kawai a kan batun hijabi, a'a, a'a, wasu kalilan ne ke da kwarin gwiwa wajen adawa da wadannan abubuwa.

"Kirkirar bambance-bambance da karkatar da jama'a" ta yadda lamarin ya wuce sabanin abokantaka da kuma yin Allah wadai da kowace kalma, ko da kuwa mai kyau ce na daya bangaren, wata hanya ce ta share fagen wajen halartar jama'a. Jagoran juyin juya halin Musuluncin, bayan ya yi bayanin hakan ya ce: hanyar fuskantar wadannan shirye-shiryen shine halartar mutane a fagen siyasa, tattalin arziki, zabe da ma batutuwan tsaro.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A fagen tsaro mutane na iya taimakawa jami'an tsaro ta hanyar zakulo makiya, domin ya zuwa yanzu an warware matsalolin tsaro da dama tare da taimakon al'umma, kuma hukumomin su iya hana aukuwar bala'o'i irin na abun da ya faru a Kerman. wanda za a iya cewa dakile makirci cikin shekaru da yawa, daidai yake da abin da ya faru.

Ya yi la'akari da inganta kasantuwar halartar al'umma da kuma taka rawa a matsayin wani muhimmin ginshiki na ingantacciyar tafiyar da mulkin kasa da kuma tabbataccen bukatu na juyin juya halin Musulunci wajen cimma manufofinsa a matsayin wata irin nasiha ga hakki da kowane mai magana aji ko na mimbari. Ya kara da cewa: Malamin addini, mai mulki, malami, malamin jami'a, mai zane, manaja, 'yan siyasa na hukuma, rediyo da talabijin, kuma kowa yana da hakkin karfafa gwiwar mutane su halarci dandalin su tsaya a ciki, duk da cewa aikin jami'an gwamnati ya fi nauyi saboda mutane a shirya suke kuma dole ne a shirya kasa don kasancewarsu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da irin gagarumin taron jama'a na cika shekaru hudu da shahadar Sardar Suleimani, da halartar al'ummar kasar a tattakin na ranar 22 ga watan Bahman da ranar Kudus, da taron ranar Ayyammullah, kamar tunawa da ranar tunawa da ranar 9 ga watan Day, a matsayin alamu karara na shirye-shiryen da jama'a suka yi na shiga wannan fage da cewa: Jama'a suna alfahari da zagayowar ranar shahadar babban kwamanda mai daraja, sun zo daga nesa don ziyartar Kerman, kuma duk da wannan mummunan lamari. Haka taron jama'a ya ci gaba da karfi da karfi da kuzari a washegarin ranar. Wannan yana nufin cewa jama'a a shirye suke kuma mu jami'ai dole ne mu shirya fage don kasancewarsu.

Dangane da abin bakin ciki na Kerman, ya ce: Hakika wannan bala'i ya girgiza al'ummarmu, duk mu dage da zargin wannan ko wancen ba, amma mun dage da gano hakikanin abubuwan da suka faru a bayan fage da murkushe su ta yadda za a magance su. In sha Allah ma'aikata masu girma da suke aiki sosai, za su iya hukunta jami’an da ke da hannu wajen aikata wannan aika-aika da kuma aikata laifin.

A bangare na karshe na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya ja hankali dangane da batun al'ummar Gaza inda yake ishara da yadda sakamakon masu hangen nesa suka fahimci sannu a hankali hasashen su zai tabbata, inda ya ce: An yi hasashen cewa, wanda ya yi nasara a wannan fagen shi ne tsayin daka da gwagwarmaya Palastinawa kuma wanda za a yi nasara a kansa shi ne tsarin mugunta la'ananne na gwamnatin sahyoniya, a yau wannan hasashen yana kan tabbatar cika.

Ya dauki watanni uku na laifuffukan yahudawan sahyoniya da kisan gilla a matsayin wani lamari da ba za a manta da shi ba a tarihi ya kuma kara da cewa: Ko bayan rugujewa da kawar da wannan gwamnati daga doron kasa, ba za a manta da wadannan laifuka ba, kuma za su shiga tarihi na daya a rana irin ta yau wasu mutane sun hau karagar mulki a wannan yanki wadanda suka kashe dubban yara tsawon makonni, amma hakurin al'ummar Palasdinu da gwagwarmaya da tsayin daka ya tilasta musu ja da baya.

Yayin da yake bayani kan alamomin shan kaye da gazawar gwamnatin sahyoniyawan bayan shafe kwanaki kusan 100 tana aikata laifukan yaki na ta'addanci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Su fa su suka ce za mu ruguza kungiyar Hamas da gwagwarmaya da kuma yunkurin al'ummar Gaza, abin da suka kasa yi har yanzu. Kuma a yau gwagwarmaya tana nan a raye, kuma a shirye take, a yayin da gwamnatin Sahayoniya ta gaji da wulakanci da nadama, kuma zafin da ke cikin mai laifi ya bugi goshinsa. (Ƙaikai ya koma kan masheƙiya)

Sun dauki wannan taro a matsayin darasi, inda suka ce: Wannan darasin ya nuna cewa dole ne layin gwagwarmaya ya zamo yana fuskantar layin zalunci, da karfi da girman kai da cin zarafi, kuma gwagwarmaya ya kamata ta kasance da zamani da shiri, kuma kada a manta da dabarar da makiya ke da ita, da taimakon Allah duk inda hali ya bayar akaiwa makiya farmaki.

Ayatullah Khamenei ya ce: In sha Allahu wata rana za ta zo da al'ummar Iran da al'ummar musulmi za su ga nasarar hakuri da gwagwarmaya da kuma dogaro ga Allah a kan makiya da shaidanun duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirga "shiriya ingantacciya" da "karfafa fahimta" a matsayin wasu bukatu guda biyu na isar da mutane zuwa fagen gwagwarmaya da tsayin daka yana mai cewa: Manufar gayyatar mutane zuwa halartar taron ita ce gudanar da harkokin Musulunci, da daukakar Musulunci, da cikakkiyan inganci mai kyau da daukaka l'umma, tare da fuskantar girman kai.

Ya kira karin ilimin jama'a a matsayin aikin masu tunani, farfesoshi, masana, dalibai da sauran bangarori masu tasiri a ra'ayoyin jama'a, ya kuma ce: Amurkawa, tare da sassaukan tunaninsu da lissafin kuskure, tare da masoyansu bayan shekaru 45, har yanzu suna ba da hujjar fuskar tsarin da a ranar 22 ga Bahman 57 aka kore shi daga wannan kasa mai tsarki ta hanyar shirin da al'umma tai masa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hannun turawan Ingila kai tsaye wajen zuwan Reza Khan kan karagar mulki inda ya kara da cewa: Tare da taimakon jami'an Birtaniya, wannan abin da mutum ya yi ya fara sauye-sauyen al'adu na al'ummar kasar bayan wasu 'yan shekaru, kuma ya kamata a kalli batun "Yaye hijabi, rufe masallatai da bukukuwan juyayi" na irin wadannan ayyuka da idon basira.

Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da katsalandan din da Birtaniyya ta yi kan zuwan Muhammad Reza kan karagar mulki da kuma juyin mulkin hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suka yi na mayar da Shah mai gudun hijira a kan karagar mulki a shekara ta 1332, ya kara da cewa: Gwamnatin Tagut ta farko da ta tsakiya da ta karshe ta hau karagar mulki tare da taimakon wasu kasashen waje ne sannan ta iya ci gaba da rayuwarta ta wulakanci, sannan kuma don neman wannan taimako ba wai man Iran kadai ta asarar ba, har ma da martaba da addini da mutuncin al'umma ga baki daya, amma a yanzu wasu mutane suna kokarin tabbatar da ingancin wannan gurbatacciyar gwamnati.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da yin bayani kan dabarun bangaren masu girman kai da cin gajiyar kasar Iran, ya kuma kara da cewa: Amurka da gwamnatin sahyoniyawan sun saba wa dabarar Imam na kawo al'umma a tsakiya filin da kuma sallama musu tutar jajircewa da gwagwarmaya, sun anfani da babbar manufar siyasa ta "fitar da al'ummar Iran daga fage" har ma a yau suna bibiyar wannan siyasa ta hanyoyi daban-daban.

Ya dauki yunkurin kaskantar da halartar mutane a munasabobi masu muhimmanci a matsayin daya daga cikin dabarar makiya na kawar da mutane daga fagen addini yana mai cewa: yin izgili da jerin gwanon arba'in, sanya shakku kan mutuntawar da mutane suke ga Shahid Sulaimani babban kwamandan kasar Iran da yankin, da kuma haifar da shakku kan halartar girman al'umma, a cikin bukukuwan addini kamar nisfu watan Sha'aban, abubuwan misalai ne na manufofin makiya na fitar da mutane daga cikin fagen addini.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Dalilin wannan kiyayyar shi ne, sun fahimci dalilin ci gaba da kuma samun karramawar Iran, da kuma fitowar ta a matsayin wani karfi mai muhimmanci a yankin, da samar da wani zurfin dabara na musamman ga tsarin, wato; Dakarun gwagwarmaya a duk fadin yankin, da kuma fatattakar dukkanin makirce-makircen juyin mulki da yake-yake, matakin kulla makarkashiyar tsaro dukansa saboda halartar al'ummar Iran a fagen.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Tabbas a inda aka hana mutane halartar waje ta ko wane hakan ya zamo dalilin jindadin makiya kamar yadda bangarori da dama na tattalin arziki iri haka suke.

Ya yi la'akari da kokarin da kafafen yada labarai na kasashen waje ke yi na kashewa mutane gwiwa musamman ma matasa daga burin nan gaba, ya kuma ce: karairayi ko wuce gona da iri, tallatawa marar anfani na shiga harkokin siyasa da zabe, da nuna wuraren da aka gaza da bayanin wahalhalu, tattalin arziki na daya daga cikin ayyukansu na tallatawa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Tabbas muna da matsalar tattalin arziki, kuma akwai rauni iri-iri kuma ana ci gaba da samunsu, kuma idan aka yi bincike da kyau, galibin wadannan raunin suna faruwa ne sakamakon rashin kasantuwar halartar mutane a can.

Ya dauki watanni uku na laifuffukan yahudawan sahyoniya da kisan gilla a matsayin wani lamari da ba za a manta da shi ba a tarihi ya kuma kara da cewa: Ko bayan rugujewa da kawar da wannan gwamnati daga doron kasa, ba za a manta da wadannan laifuka ba, kuma za su shiga tarihi na daya a rana irin ta yau wasu mutane sun hau karagar mulki a wannan yanki wadanda suka kashe dubban yara tsawon makonni, amma hakurin al'ummar Palasdinu da gwagwarmaya da tsayin daka ya tilasta musu ja da baya.

Yayin da yake bayani kan alamomin shan kaye da gazawar gwamnatin sahyoniyawan bayan shafe kwanaki kusan 100 tana aikata laifukan yaki na ta'addanci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Su fa su suka ce za mu ruguza kungiyar Hamas da gwagwarmaya da kuma yunkurin al'ummar Gaza, abin da suka kasa yi har yanzu. Kuma a yau gwagwarmaya tana nan a raye, kuma a shirye take, a yayin da gwamnatin Sahayoniya ta gaji da wulakanci da nadama, kuma zafin da ke cikin mai laifi ya bugi goshinsa. (Ƙaikai ya koma kan masheƙiya)

Sun dauki wannan taro a matsayin darasi, inda suka ce: Wannan darasin ya nuna cewa dole ne layin gwagwarmaya ya zamo yana fuskantar layin zalunci, da karfi da girman kai da cin zarafi, kuma gwagwarmaya ya kamata ta kasance da zamani da shiri, kuma kada a manta da dabarar da makiya ke da ita, da taimakon Allah duk inda hali ya bayar akaiwa makiya farmaki.

Ayatullah Khamenei ya ce: In sha Allahu wata rana za ta zo da al'ummar Iran da al'ummar musulmi za su ga nasarar hakuri da gwagwarmaya da kuma dogaro ga Allah a kan makiya da shaidanun duniya.