Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Janairu 2024

07:23:30
1427834

An kai hari da wuka a kan limamin masallacin Fatih da ke Istanbul

Wani mutum ya kaiwa limamin masallacin Fatih dake Istanbul hari da wuka.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: An kai wannan harin ne da yammacin ranar Litinin bayan sallar Magriba, inda aka kai wa Ghalib Avista limamin jama'a na masallacin da Bilal Erdam wani ma'aikacin masallacin Fatih da ke Istanbul hari da wuka inda suka samu raunuka sakamakon wannan harin.