Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Janairu 2024

06:09:59
1427817

Iran Ta Gargadi Amurka Dangane Da Duk Wani Matakin Tabarbarewar Tsaro A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Iran ta yi gargadi kan duk wani mataki na tunzura Amurka da kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a yankin

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Yayin da yake yin watsi da ikirarin Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da tekun Bahar Rum, jakadan kasar Iran a MDD ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana mai gargadi kan duk wani mataki na tsokana ko rashin da'a da Amurka za ta dauka, da ka iya jefa yankin cikin hadari zaman lafiya da tsaro, Kwamitin Sulhun na son yin aiki da alhakin da ya rataya a wuyansa na magance musabbabin halin da ake ciki a tekun Bahar Rum.