Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

5 Janairu 2024

17:30:39
1426882

Iran: Ma'aikatar Yaɗa Labaran Iran Game Da Lamarin Ta'addancin Kerman; Ana Cigaba Da Kama Masu Hannu A Harin Ta'addancin Kerman

Daga cikin 'yan ta'addar kunar bakin wake guda biyu da suka mutu, daya dan asalin kasar Tajikistan ne kuma har yanzu ba a tantance ko wanene dan ta'adda na biyun ba.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowo daga kamaf labarai na Alquds cewa: Bayan gano jami'an da ke jigilar 'yan ta'addan zuwa cikin kasar, an fara fara kame jami'an da aka ambata a yammacin ranar da lamarin ya faru.

A safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, an gano gidan da matattun ‘yan ta’addan biyu suka yi amfani da shi a unguwar Kerman, sannan an gano wasu 2 da ke dafa masu da kuma samar da kayayyakin gidan da aka ce an kama tare da kama su.

A ci gaba da kai farmakin, an gano mutane 9 daga cikin kungiyar masu tallafawa 'yan ta'addan tare da kame su a larduna 6 na kasar. Wannan aiki ba shakka zai ci gaba har sai an kama mutum na karshe da ke da hannu wajen tallafawa masu aikata laifuka ta kowace hanya da kuma ko wane mataki.

Rashin fitar da sanarwa har zuwa wannan lokaci ya faru ne sakamakon gano wasu na'urori masu fashewa a gidan 'yan ta'addar, wanda hakan na iya nuni da yiwuwar kasancewa tare da zuwan wasu jami'ai don daukar abubuwan fashewa da kuma amfani da su a wasu wuraren. Wasu daga cikin na'urorin da aka samu sun hada da: Riguna 2 na fashewar bam, na'urorin sarrafa su daga nesa guda 2, bama-bamai 2, harsasai dubu da dama da aka yi amfani da su wajen bama-bamai, da wayoyi da aka tanada domin rigunan bamaman da kuma adadi na sinadarin fashewar bom din.