Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

5 Janairu 2024

17:04:15
1426878

Sayyid Hassan Nasrallah: Amurka Ba Tana Fuskantar Gwamnati, Ko Sojoji, Gwagwarmaya A Kasar Yemen Kawai Ba Ne...

Sayyid Nasrallah dangane da kisan da aka yi wa Al-Aroori a birnin Beirut: akwai martani babu makawa, lamari ne na figen yaki.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a wajen taron tunawa da shahidan Haj Muhammad Yaghi daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah.

Sama da sojojin yahudawan sahyoniya dubu takwas ne ke kwance a asibitoci takwas kacal na gwamnatin sahyoniyawan

Makiya ba su ikrari da kashe ko raunata sojojinsu, kuma boye labarai masu tsanani na irin hasarar da suka yi na daga cikin manufofinsu.

Wasu masana na gwamnatin sahyoniyawan sun ce barnar da aka sanar ya ninka adadin da aka sanar sau uku.

Abin da ke faruwa a yankin fagen daga na arewa, tozarta ce ta makiya sahyoniya ta hakika.

Sayyid Nasrallah dangane da kisan da aka yi wa Al-Aroori a birnin Beirut: akwai martani babu makawa, lamari ne na figen yaki.

A baya, muna da wata dabara cewa idan aka kashe wani a Siriya, za mu mayar da martani a fagen Lebanon, amma lokacin da aka kai hari a cikin karkara, yanayin ya bambanta.

Nasrullah: Ba mu ce za mu maida martani a wani guri a lokacin da ya dace ba, amma fagen shi zai bayarda damar hakan.

Gwamnatin Amurka ta damu matuka game da fadada da'irar yaki a yankin saboda ba ta da wata sha'awa a cikinsa.

Amurka ba ta son fadada yakin saboda tana shagaltuwa a bangaren Ukraine da kuma kawar da shirye-shiryen Rasha bisa dabarun yaki.

Sayyid Hasan Nasrallah: Mazauna yahudawan sahyoniya dubu 300 ne suka rasa matsugunansu

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon yace Mazaunan duk sojoji ne ba 'yan kasa fararen hula ba.

A ayyukan kungiyar Hizbullah na soja, muna kai wa sojoji hari, har ma muna kai hari kan jami'ai da motocin sojoji a matsugunansu.

A sakamakon firgici mazauna wannan yanki sun bar gidajensu sun bar yankin.

Kafofin yada labaran Amurka sun ambato jami'an yahudawan sahyoniya na cewa matsugunan su 230,000 ne suka bar yankin.

Jami'an yahudawan sahyoniya sun kuma yi magana game da samuwar bakin haure 300,000.

Sayyid Hassan Nasrallah: Ina ce wa da Amurka, ba kina fuskantar wata gwamnati, ko sojoji, da kungiyar gwagwarmaya da kuma kungiyar soji a kasar Yemen kawai ba ne.

Kina fuskantar miliyoyin Yamanawa ne wanda ba za su daina ba, za su kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da masu ba da kayayyaki ga Isra'ila.

Suna da daraja domin sun yi imani da Allah kuma gareshi suka dogara.

Ya 'yan kasar Yemen suna masu alfahari kuma wannan yana daga cikin falalar Jihadi da kuma tsayuwa da sukai wajen marawa Palastinu da ake zalunta.

Sayyid Hassan Nasrallah yayin da yake jawabi ga iyalan shahidan:

Ina ganin maganganinku kan shahadar masoyanku. Idan ba don ƙarin matakan tsaro ba, wanda sun kara karuwa da Ina so in sumbace hannayenku.