Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

3 Janairu 2024

18:52:46
1426423

Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Bayan Harin Ta'addanci A Kerman

"Wannan Musibar Akwai Matsanancin Martani Da Zai Biyo Bayanta Insha Allah “Masu taurin kai su sani cewa sojojin tafarkin haske na Suleimani ba za su lamunta da mugunta da laifukansu ba. Su wadannan masu aikata laifuka su sani cewa tun a yanzu za su fuskanci dankwafarwa da hukunci na adalci”.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Khamenei ya fitar da sakon ta'aziyya bayan shahadar wasu gungun maziyarta a hubbaren Shahid Suleimani a wani harin ta'addanci da aka kai kan hanyar Gulzar Shuhada a garin Kerman.

Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka:

بسم الله الرّحمن الرّحیم

Azzaluman makiya masu laifi ga al'ummar Iran sun sake haifar da wani bala'i tare da shahadar dimbin al'umma a yankin Kerman da kuma falfajiyar mai kamshi ta kaburburan shahidai.

Al'ummar Iran sun yi alhini tare da alhinin mutuwar tsokar jukkunansu da 'yan uwansu da dama. Masu aikata laifuka masu taurin zuciya sun kasa jurewa soyayya da sha'awar da jama'a ke yi na ziyartar haramin babban kwamandansu Qassim Suleimani. Su sani cewa sojojin tafarkin haske na Suleimani ba za su amince da mugayen ayyukansu da aikata laifukansu ba. Dukkan Hannayen da suka dulmiya da jinanen wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da kuma gurbatattun kwakwalwa masu barna da suka kai su ga wannan ɓatan, tun daga yanzu zasu fuskanci da hukunci da kawarwa da dankwafarwa na adalci. Kuma Su sani wannan bala'in da suka aukar martani mai tsanani zai biyo bayan shi Insha Allah.

Ina jajantawa iyalan wadanda suka rasu tare da yi musu addu'ar Allah ya basu hakuri da juriya. tsarkakakkun ruhin shahidai, in sha Allahu, su zamo baki ga shugabar duniya biyu kuma uwar shahidai Sayyida Siddiqah Tahirah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta. Ina jajanta wa wadanda suka jikkata kuma ina yi musu addu'ar samun lafiya.

Sayyid Ali Khamenei

3 ga Janairu, 2024