Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

2 Janairu 2024

14:22:29
1426064

Adadin Shahidan Gaza Ya Kai Mutane 22185

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta kuma jaddada cewa adadin wadanda suka jikkata ya kai 57,035.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowo daga kamfanin dillancin labarai na Qodsnewsagency cewa: Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwarta ta baya-bayan nan cewa adadin shahidai a Gaza ya karu zuwa 22,185 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta kuma jaddada cewa adadin wadanda suka jikkata ya kai 57,035.

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata sojojin yahudawan sahyuniya sun aikata kisan gilla da wasu laifukan taaddanci guda 15 a yankin Zirin Gaza inda a sakamakon haka aka kara samun mutane 207 da suka yi shahada tare da jikkata wasu 338.