Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

2 Janairu 2024

14:10:47
1426061

An kai hare-hare 7 kan sansanonin Amurka a cikin sa'o'i 24 kacal

Ana Ƙara samun matsin lamba gwagwarmayar Iraqi kan abubuwan da ke faruwa a Gaza


A safiyar yau talata gwagwarmayar Musulunci ta Iraki ta kai hari kan sansanin Al-Khadra na Amurka da ke kasar Siriya da wasu jiragen yaki marasa matuki.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Bayan sa'a guda da wannan an kara kai hari kan sansanin sojojin Amurka da ke kusa da filin jirgin sama na Erbil a Iraki.

A yammacin yau din nan ne dai bayan azuhur aka kara kara kai hari kan sansanin sojojin mamayar Amurka da ke al-Shadadi a kasar Siriya.

Nan da nan bayan harin da aka kai kan sansanin al-Shadadi, an kuma kai hari kan sansanin Al-Maliki.

Mintuna kadan bayan wadannan hare-hare guda biyu, mayakan Islama na kasar Iraki sun sanar da cewa, sansanonin Amurkan da ke Remilan suma an kai musu harin makamai masu linzami.

A daren jiya ma dai dakarun kasar Iraki sun bayar da rahoton wani harin roka da aka kai kan sansanin sojojin Amurka da ke Ain al-Asad a arewa maso yammacin kasar Iraki. Wanda Nan take kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sansanin sojin Amurka da ke Koniko da ke Deir Ezzor a gabashin kasar Siriya shi ma an kai hari da makaman roka.

A cikin wannan bayani, gwagwarmayar Iraki ta sanar da cewa: Ta hanyar kai hari kan sansanonin Amurkawa a Iraki da Siriya fiye da sau 100, mun bayyana wa dakarun Amurka cewa, goyon bayan da takeyi na kashe-kashen da ake gudanarwa ta hannun gwamnatin yahudawan sahyoniya ga al'ummar Gaza yana da girma sosai.