Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Janairu 2024

15:14:20
1425759

“Ruhiyya, Sadaukarwa, Da Riko Da Wilaya” Na Daga Cikin Sifofin Da Sayyidah Zahra (a.s) Da Imam Khumaini (a.s) Da Haj Qasim Suleimani Sukai Tarayya Akai

Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya jaddada cewa: Sayyida Zahra (AS) tana kan kololuwar ruhin Imani Sakamakon wannan ruhiyyar ya zamo shine jure daukar nauyi. Mafi girman nauyi kuwa shi ne sadaukar da kai kuma kololuwar sadaukarwa da ta kasance a wajen Sayyida Zahra (AS).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: an gudanar da bukukuwan maulidin Sayyida Fatima (S) da kuma gudanar da ranar mata mai taken "Zahra'aul Adhar, Abin Koyi Na Ruhi Da Sadaukarwa Da Riko Da Wulaya" tare da halarta Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) da dalibai daga kasashe daban-daban a jami'ar Ahlul Baiti (AS). Wanda aka gudanar da taron a Yau ranar litinin 1 ga watan Junairu shekara ta 2024.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) a yayin bikin, ya taya iyaye mata da mata murnar zagayowar wannan rana, ya bayyana cewa: Akwai munasabobi da dama a wannan rana, mafi muhimmanci daga cikinsu ita ce haihuwar Sayyidah Fatimah mai albarka (S.A.W) kuma a wannan rana, mata da uwaye su ne mizanin soyayya, tausayawa da kyautatawa na Ubangiji.

Ayatullah Ramezani ya kara da cewa: Har ila yau, wannan rana ta zo daidai da ranar haihuwar wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khumaini (RA) da shahadar kwamandan zukata Haj Qasim Suleimani da Abu Mahdi Al-Muhandis, wanda daya ne daga cikin mataimaka da abokan wannan babban kwamanda.

Babban magatakardar majalisar duniya ta Ahlul Baiti (a.s) ya ci gaba da bayyana cewa "Ruhiyyar Imani da sadaukar da riko da wilaya" na daga cikin sifofin da Sayyidah Fatima Zahra (a.s) da Imam Khumaini (a.s) da Hajj Qasim Suleimani Sukai musharaka akai inda ya ce: "Ruhaniya ta mutum bisa dogaro da ga gaskiyar gaibu da Malakutiyya tana sanya karkatuwa zuwa ga dabi'u masu tsarki da al'amuran na fidirar halitta.

Idan aka koma akayi nazari aya ta 39 a cikin suratu Mubarakah Al-Dukhan da ke cewa «ما خَلَقناهُما إِلّا بِالحَقِّ وَلکِنَّ أَکثَرَهُم لا یَعلَمونَ»

“Ba mu halicce su ba face da gaskiya, amma da yawansu ba su sani ba”. Ya bayyana cewa: Mutum halitta mai ma'ana, Da yawa suna kula da hakan, ko suna sane ko ba su sani ba, wani lokacin ana lullube wannan gaskiyar, amma dukkansu suna da ma'ana. Wannan kuma ya dogara ne akan halitta ga haƙikane ba wai ya haɗa da mutane ba har ma da dukan duniya, kuma dukansu an halicce su bisa ga gaskiya, kuma babu abin da aka halicce shi bisa bata.

 Ayatullah Ramezani ya ce: Ruhi mai dogaro da imani ya ginu ne a kan imani ga gaibi, imani da Allah, imani da lahira, imani da littattafan sama, imani da annabawan Ubangiji, da imani da wahayi. Tushen da tsarin ruhi da mutum yake son matsawa zuwa gare shi yana kan imani da bangaskiya ne.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya ci gaba da cewa: A yau, a duniyar 'yanci da na duniya na yammaci, ba a maganar ruhi ta wannan ma'ana, kuma ana maganar ruhi da cikakkiyar sifar ma'ana ne. Da ta ginu akan cewa Babu bukatar Allah ya kasance a cikin wannan ruhi, kuma ko da ta hanyar musunta Allah ne to suna kawo maganar ruhiyya.

Memba na Majalisar Kwararru na Jagoranci ya kira daukar nauyi mafi mahimmanci daga sakamako na ruhaniyya mai karkata zuwa ga bangaskiya kuma ya kara da cewa: Lokacin da mutum ya kai ga wannan ruhi, yakan kai wani nau'i na nutsuwa kuma ya zamo Shine zaman lafiyar ɗan adam a yau. Wasu mutane neman wannan zaman lafiya da nutsuwa daga abubuwa masu saukaka ciwo da sauran batutuwa, amma wannan zaman lafiya da nutsuwar ba zai samu ba sai dai idan mutum ya sadu da Maɗaukakin Sarki, da Ubangiji Masoyi abun kauna. Idan wannan alaka ta faru ita ce zata haifar da nutsuwa kawai.

 Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa, ladabin ma'abocin imani ladabi ne na musamman kuma wannan ladabi na musamman ya zo a cikin ayyukansa da dabi'unsa da kuma maganganunsa yana mai cewa: Ruhin imani yana kai mutum zuwa ga hakikanin mutum. Kuma Allah Ubangijin talikai ya kira yi dukan ’yan Adam zuwa ga wannan ruhi.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya jaddada cewa: Sayyida Zahra (AS) tana kan kololuwar ruhiyyar Imani. Sakamakon wannan ruhi shine ya kaita ga daukar mafi girman nauyi ta da sadaukarwa da kai kuma kololuwar sadaukarwa ta kasance ga Sayyida Zahra (AS) ne.

Ya ce: Sayyidah Zahra (a.s) mutum ce wanda ruhinsa ya ginu a kan imani da Allah kuma wannan ruhi yana kan kololuwar sa. Idan mutum ya kai ga ruhaniya a zahiri, mafi mahimmancin sakamako a cikin rayuwar ɗan adam shine zama cikin aminci ne da nutsuwa, tsaro da daukar nauyi.

Ayatullah Ramezani ya ci gaba da cewa Sayyida Zahra (a.s) ta damu da shiryar da wasu da magance matsalolin wasu mutane da kawar da talauci da bauta, ya kuma bayyana cewa: Daya daga cikin sifofin Sayyida Zahra (a.s) ita ce riko da wilaya, bata bar Imam Ali (AS) shi kadai ba a cikin mafi tsananin yanayi, kuma bata rabu da shi ko da na dan wani lokaci.

Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa Imam Khumaini (RA) dalibi ne na mazhabar Fatimiyyah, mutum ne mai ruhiyya, mai sadaukar da kai mai riko da wilaya, ya kara da cewa: Shi ma Hajj Qasim yana da wadannan siffofi guda uku. Ya kasance yana son limamai, ya kasance mutum mai rikon amana, abin dogaro da sanin makamar aiki, kuma ya sadaukar da kansa wajen yakar ta'addanci, ya ba da jininsa tsarkakakke a matsayin kyauta domin al'ummar bil'adama su samu kwanciyar hankali da tsaro. Ya jagoranci yaki da ta'addanci a wannan zamani kuma ya sami wannan matsayi kuma ya shahara a duniyar yau, kuma yanayin da akai jana'izar sa ya zamo alami ne da taba samun irinsa ba a tarihin.

Ya kamata a ambaci cewa a cikin wannan bikin, daya daga cikin daliban Pakistan ya karanta wakoki kuma Mista Rezaei ya rera wakar yabo.