Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Janairu 2024

12:39:16
1425698

Al-Qassam Ɓangaren Soji Na Kungiyar Hamas Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Isra'ila

Al-Qassam Ɓangaren Soji Na Kungiyar Hamas Sun Sanar a jiya Lahadi cewa mayakanta sun harbo wani jirgin leken asiri na Skylark 2 wanda ke aikin leken asiri ga makiya yahudawan sahyoniya a Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a jiya Lahadi ne dakarun kungiyar Al-Qassam reshen kungiyar Hamas sun harbo wani jirgin leken asiri mai suna "Skylark 2" wanda ke aikin leken asiri ga makiya yahudawan sahyoniya a Beit Lahia Arewacin zirin Gaza.

A sanarwar da rundunar ta Al-Qassam ta fitar ta ce: "Rundunar Al-Qassam Brigades ta harbo wani jirgin leken asiri na Skylark 2 da ke cikin tawagar leken asirin makiya a Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza."

Da sanyin safiyar yau ne dakarun Al-Qassam suka sanar da cewa mayakanta sun kai hari kan wani jirgin sama mai saukar ungulu na Apache na makiya Isra'ila a kudancin unguwar Al-Zaytoun da ke birnin Gaza da makami mai linzami samfurin SAM 7.

Al-Qassam ta ce mayakan nata sun kuma kai hari kan dakarun yahudawan sahyoniya na musamman da ke gabashin yankin Al-Tuffah da ababen fashewa da makamai masu linzami tare da yin arangama da su da manyan bindigogi, sannan kuma sun yi luguden wuta kan wasu tawagogi biyu na motocin mamaye da sojoji a birnin Khan Yunus Kudancin Zirin Gaza.

An kuma kai hari kan wasu motocin mamaya guda biyar a yankunan Al-Tuffah da Al-Daraj, da wasu bama-bamai na “Shawaz” da kuma makamin “Al-Yassin 105”.