Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

1 Janairu 2024

11:55:52
1425689

Shugaban Makarantar Hauza Na Iran Ya Gana Da Shaikh Zakzaky

Ayatullah Arafi, shugaban makarantar hauza ta Iran, ya yaba da kokarin Shaikh Zakzaky na yada al’adu da koyarwar Musulunci tsantsa da kuma koyarwa da al’adun juyin juya halin Musulunci a Nijeriya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Arafi shugaban makarantar hauza ta Iran ya yaba da kokarin Shaikh Zakzaky na yada al’adu da koyarwar Musulunci tsantsa da kuma tushen koyarwar al’adun juyin juya halin Musulunci a Najeriya.

Shugaban na makarantun hauza ta Iran ya gana kuma ya tattauna da Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Najeriya a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba.

A wannan taron, Shaikh Zakzaky ya gabatar da rahoto kan ayyukan al'adu da Musulunci a Najeriya da kuma batutuwan da suka shafi duniyar Musulunci da Afirka.

Malamin na Najeriya ya dauki nasarar harkar Musulunci da ci gaban al'adu a Najeriya da Afirka a matsayin abin koyi da marigayi Imam Khumaini (RA) da kuma juyin juya halin Musulunci na Iran ya kuma bayyana cewa, juyin juya halin Musulunci yana ci gaba a karkashin jagorancin Ayatullah Imam Sayyid Ali Khamene'i DZ kuma muna masa addu’ar Allah ya kara masa lafiya da nasara”.

A cikin wannan taro, Ayatullah Arafi shugaban makarantar hauza na kasar Iran, ya yaba da kokari da jajircewa tare da sadaukarwar Sheikh Zakzaky na yada al'adu da koyarwar Musulunci tsantsa da kuma bahasin al'adun juyin juya halin Musulunci a Najeriya, tare da yi masa fatan lafiya da nasara, tare da bayyana hakan da fatan gwamnatin Najeriya za ta ba da hadin kai tare da daukar matakan da suka dace. Ya kuma yi jinjina ga ruhin shahidan Musulunci, tsayin daka da gwagwarmaya na Musulunci, jaruman Gaza da Nijeriya, musamman tsarkakan rayuka da abokan huldarsu.