Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

31 Disamba 2023

11:23:20
1425364

Jagora: Ikhlasi, Basira, Hankali Da Halayya Sune Sirrin Nasarar Haj Qasim Suleimani Na Farfado Da Fafutukar Gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a wata ganawa da iyalan shahidi Haj Qassem Suleimani: Muhimmiyar rawa da hidimar Haj Qassem Suleimani ita ce farfado da fagen gwagwarmaya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i DZ a yayin ganawarsa iyalan shahid Haj Qassim Sulaimani inda ya ce a cikin bayanansa: Muhimmiyar rawa da hidimar Haj Qassem Suleimani ita ce farfado da fagen gwagwarmaya a yankin. Tsayin daka da gwagwarmaya na tsawon watanni kusan uku a Gaza yana faruwa ne saboda samuwar fagen gwagwarmaya; Shahidi Suleimani ya yi kokari matuka wajen farfado da bangaren tsayin daka da gwagwarmaya tare da gudanar da wannan aiki cikin ikhlasi da hikima da kyawawan halaye.